Gaskiya Ta Fito kan Zargin Zuwan Sojojin Kasar Faransa Najeriya
- Rundunar tsaron Najeriya ta ce labarin cewa sojojin Faransa za su kafa sansani a Najeriya ba gaskiya bane kwata kwata
- Mai magana da yawun rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana zargin a matsayin kirkirarriyar ƙarya
- Manjo Janar Buba ya yi kira ga al'umma da su yi watsi da jita-jitar da ya ce tana ɗauke da manufar ɓata suna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Rundunar tsaron Najeriya ta musanta rahotanni da ke cewa sojojin kasar Faransa sun isa Maiduguri domin kafa sansanin soji a yankin Arewa maso Gabas.
A cikin wata sanarwa da Manjo Janar Edward Buba ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa zargin ba gaskiya ba ne kuma yana da hadari ga tsaron ƙasa.
Punch ta wallafa cewa martani ya biyo bayan wani bidiyo da wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Mahdi Shehu ya wallafa a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mahadi Shehu ya wallafa bidiyo a X yana zargin cewa wasu sojojin Faransa sun iso jihar Borno domin fara aikin kafa sansani.
Sojoji sun karyata zuwan Faransa Najeriya
Daraktan yada labaran rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya ce an jawo hankalinsu kan wani rahoto a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu sojojin Faransa sun isa Maiduguri.
“Rundunar sojojin Najeriya na sanar da al’umma a bayyane cewa wannan labarin ƙarya ne, ba gaskiya ba ne, kuma yana da nufin ɓata suna.
A baya-bayan nan, Hafsun Tsaro, Janar Christopher Musa ya tattauna kan wannan batu a wurare daban-daban, inda ya musanta irin waɗannan jita-jitar."
- Manjo Janar Edward Buba
Rundunar tsaro ta yi kira ga 'yan Najeriya
New Telegraph ta wallafa cewa Rundunar tsaron ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da labarai marasa tushe da ake yadawa da nufin tayar da rikici.
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar sojoji za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kare ƙasa da kuma tabbatar da haɗin kan Najeriya cikin ƙwarewa.
A ƙarshe, Manjo Janar Edward Buba ya yi kira ga kafafen yada labarai da sauran jama’a da su taimaka wajen yada gaskiya da watsi da labaran karya.
Najeriya ta kulla yarjejeniya da Faransa
A wani rahoton, kun ji cewa Najeriya ta kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai da Faransa domin habaka tattalin arziki.
Legit ta rahoto cewa an kulla yarjejeniyar ne a yayin wata ziyara da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai kasar Faransa a kwanakin baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng