An ba Kasashen Nijar da Kasashe 2 Watanni 6 Su Sake Nazarin Ficewa daga ECOWAS

An ba Kasashen Nijar da Kasashe 2 Watanni 6 Su Sake Nazarin Ficewa daga ECOWAS

  • ECOWAS ta amince da ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikin kungiyar kamar yadda su ka nema
  • Kasashen uku za su kammala fita daga cikin ECOWAS a watan Janairu, amma duk da haka an ba su kofar watanni shida don sake nazari
  • Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Touray, ya bayyana cewa an kuma samar da kwamitin da zai bibiyi yadda za a kammala ficewar kasashen

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kungiyar ECOWAS ta ba Burkina Faso, Mali, da Nijar wa’adin watanni shida, daga 29 ga Janairu zuwa 29 ga Yuli 2025, don sake nazarin matsayinsu na ficewa.

Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Touray, ya sanar da wa’adin watanni shida a ranar Lahadi a Abuja, bayan taron kolin shugabannin kungiyar karo na 66.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta wuce gona da iri, bashin da aka karbo ya haura iyaka da N4trn

Tinubu
ECOWAS ta amince da ficewar kasashe 3 daga cikinta Hoto: : @ecowas_cedeao
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ECOWAS na fatan kasashen da ke karkashin mulkin soja za su sake nazari da zummar dawo wa cikin kungiyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ECOWAS ta kara amince da ficewar kasashe 3

BBC Hausa ta ruwaito cewa hukumar ECOWAS ta amince da ficewar jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso wajen tabbatar da ficewarsu daga cikin kungiyar.

“Hukumar ta amince da cewa, bisa tanadin sashe na 91 na kungiyar da aka gyara, wadannan kasashe uku za su daina kasancewa mambobin ECOWAS daga 29 ga Janairu 2025.

ECOWAS ta fara sallama da Nijar da kawayenta

Kungiyar ECOWAS ta fara shirye-shiryen ficewar kungiyoyin Nijar, Mali and Burkina Faso daga cikin kungiyar a shekarar 2025.

Shugaban hukumar kula da ECOWAS, Omar Touray ya ce;

“Hukumar ta umarci Majalisar Ministoci ta kira wani Taro na Musamman a cikin rubu’i na biyu na 2025 domin tattauna da kuma amincewa da tsare-tsaren rabuwa da kuma shirin gaggawa da zai shafi alakar siyasa da tattalin arziki tsakanin ECOWAS da Jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Mali, da Burkina Faso.”

Kara karanta wannan

'Saurin me ake yi?" Dattawan Arewa sun shawarci gwamnati kan kudirin harajin Tinubu

ECOWAS ta tattauna batutuwa 30 a Abuja

A wani labarin, kun ji cewa ministocin kungiyar ECOWAS sun hallara a babban birnin tarayya Abuja, inda su ka tattauna batutuwa akalla guda 30 da su ka shafin yankin.

Gaba-gaba daga cikin abubuwan da aka zauna a kai, akwai batun ficewar kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso daga cikin kungiyar ECOWAS, tattalin arziki da tsaron yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.