'Jagoran Kisan Sarkin Gobir': Sojoji Sun Cafke Shugaban Ƴan Bindiga, Bako Wurgi

'Jagoran Kisan Sarkin Gobir': Sojoji Sun Cafke Shugaban Ƴan Bindiga, Bako Wurgi

  • Sojojin Najeriya sun cafke fitaccen shugaban 'yan bindiga Bako Wurgi, wanda ake zargin shi da kisan sarkin Gobir a jihar Sokoto
  • An rahoto cewa sojojin sun cafke Bako Wurgi a asibitin Shinkafi da je jihar Zamfara, inda yake jinyar wasu raunukan da ya samu
  • Yayin da aka baza komar kama yaransa, an ce kama dan bindigar alama ce ta nasarar da sojoji ke samu a yaki da ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Sojojin runduna ta daya sun kama shugaban ‘yan ta’adda da dillancin makamai, Bako Wurgi, wanda aka fi sani da Baka NaGarba.

Ana zargin Bako Wurgi ne ya shirya yadda aka kashe Sarkin Gobir, Alhaji Isa Mohammad Bawa, a jihar Sokoto.

Sojojin Najeriya su cafke dan bindigar da ya kitsa kisan sarkin Gobir
Sojojin Najeriya sun cafke hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bako Wurgi a Zamfara. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji sun cafke shugaban 'yan bindiga

An kama dan ta'addan a ranar 14 ga Disamba bayan rahoton leƙen asiri ya tabbatar yana jinya a asibitin Shinkafi, jihar Zamfara, a cewar rahoton Zagazola Makama.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun shiga uku: Hafsan tsaro ya tura dakaru na musamman, ya fadi shirinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce ya samu raunuka sakamakon arangama da wata ƙungiyar ‘yan bindiga kafin sojoji su cafke shi.

Sojoji sun kama mutum ɗaya da ya taimaka wajen kai Bako Wurgi asibiti, yayin da abokan tafiyarsa biyu suka tsere.

Hannun Bako Wurgi a kisan sarkin Gobir

An sace Sarkin Gobir a ranar 9 ga Yuli, 2024, sannan aka kashe shi ranar 22 ga Agusta bayan yarjejeniyar fansa ta rushe.

Rahotanni sun bayyana cewa Bako Wurgi ya taka muhimmiyar rawa a sacewa da kisan sarkin Gobir bayan an gaza kai masu kudin fansarsa.

An kuma rahoto cewa Baka NaGarba, wanda ya kware a dillancin makamai a ƙasa da ƙasa, ya na da alaƙa da Bello Turji ta bangaren kakansa.

An jinjinawa sojoji kan kama Bako Wurgi

An ce dansa, Sani Duna, yana taimakawa Bello Turji ta hanyar kai masa bayanai ta babur, yana kuma nuna alaƙarsu ta iyali a cikin tawagar 'yan bindigar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fara gwajin bama bamai a Zamfara, yaran Bello Turji sun mutu

Kama Bako Wurgi babban ci gaba ne a kokarin da ake yi na magance ta’addanci da ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma.

A halin yanzu, Bako Wurgi yana tsare a wurin da ba a bayyana ba, yayin da ake farautar sauran abokan tafiyarsa.

Mazauna jihohin Sakkwato, Kebbi, da Zamfara sun yaba da wannan aiki, suna fatan hakan zai rage tasirin ta’addanci a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.