"Dole Mu Farka," Sarki Muhammadu Sanusi Ya Faɗi Haɗarin da Arewa Ke Ciki a Najeriya

"Dole Mu Farka," Sarki Muhammadu Sanusi Ya Faɗi Haɗarin da Arewa Ke Ciki a Najeriya

  • Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda Arewa ta zama koma baya a fannin ci gaba
  • Basaraken ya bukaci masu ruwa da tsaki a Arewa su maida hankali wajen bunkasa harkokin ilimi da noma domin ci gaban yankin
  • Sanusi ya ce ƴan Kudu sun rika sun yi wa Arewa fintinkau ta yadda ko da an raba Najeriya ba za su ji komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya koka kan yadda Arewaci ta koma baya matuka a fannin ci gaba musamman a batun da ya shafi ilimi da noma.

Basaraken ya bayyana cewa rashin ci gaba ya sa ƴan Arewa ke rayuwa cikin wahala, inda ya bukaci shugabanni su farka daga barci.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da sabuwar adawa mai zafi daga Arewa kan kudurin gyaran haraji

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Muhammadu Sanusi II ya koka kan yadda Arewa ta zama koma baya a fannin ci gaban zamani Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Sarki Sanusi ya damu da rashin cigaban Arewa

Sanusi II ya faɗi haka ne ranar Asabar wurin taron tunawa da zuwan jagoran ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Ibrahim Nyass Najeriya karo na 50 a Jos, jihar Filato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin, wanda shi ne babban bako mai jawabi a wajen taron, ya ce Arewa ta kasa cin moriyar dimbin al’ummar da Allah ya ba ta, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce galibin mutanen Arewa manoma ne amma har yanzu ba su da ilimin fasahar noman zamani.

'Arewa na cikin haɗari" - Sanusi II

"Arewa muna cikin haɗari, yau idan aka raba Najeriya akwai wuraren da in sun tafi, sun tafi kenan, suna da filayen jiragen sama da na ruwa, layin dogo da masana'antu.
"Suna da fasahar zamani, suna da ruwa, suna da lantarki, gaba ɗaya lantarkin ƙasar nan tana can, mu (a arewa) ne muke da shi? Me muka bar wa ƴaƴanmu?"

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya roki afuwar al'umma kan kiran Sanusi II da tsohon sarki

- Muhammadu Sanusi II.

Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki a Arewa su zuba jari a fannin ilimi da noma domin ci gaban yankin da al’ummarsa, ya kara da cewa dole ne Arewa ta farka.

Muhammadu Sanusi ya gana da gwamnan Filato

A wani labarin, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara ta musamman a jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci Gwamna Caleb Mutfwang na jihar a gidan gwamnati inda suka zanta kan wasu batutuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262