Sojoji Sun Yi Galaba kan 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi namijin ƙoƙari bayan sun samu kiran gaggawa kan harin ƴan bindiga a jihar Taraba
- Sojojin sun bi sahun ƴan bindigan a ƙauyen Manzala da ke ƙaramar hukumar Yorro inda suka kuɓutr da mutane uku da suka yi garkuwa da su
- Bayan kuɓutar da mutanen, sojojin sun kuma ci gaba da yin sintiri domin daƙile barazanar ƴan bindiga a yankunan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Whirl Stroke sun ceto wasu mutane uku da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Taraba.
Dakarun sojojin sun ceto mutanen ns a ƙauyen Manzala da ke ƙaramar hukumar Yorro ta jihar Taraba.
Sojoji sun yi nasara kan ƴan bindiga
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da muƙaddashin daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na rundunar, Olubodunde Oni ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce a ranar 13 ga watan Disamban 2024, sojojin sun samu kiran gaggawa kan harin ƴan bindiga a ƙauyen.
Bayan sun isa ƙauyen, sun bi sahun ƴan bindigan inda suka samu nasarar ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su.
Olubodunde Oni ya ce ce tuni aka sada mutanen da aka yi garkuwa da su waɗanda aka ceto da iyalansu.
Ya ce daga nan dakarun sojojin suka gudanar da sintiri a yankunan da ke da tsaunuka a ƙananan hukumomin Ardo-Kola da Yorro, domin kawar da duk wata barazana.
Sojoji sun cafke ɗan fashi
Bugu da ƙari, sojoji a ranar 12 ga Disamba, 2024, yayin da suke gudanar da sintiri a kan hanyar Takum Katsina Ala, sun ci karo da ƴan fashi da makami a kusa da kasuwan Shanu a cikin garin Takum.
Cikin gaggawa suka cafke wani da ake zargin ɗan fashi da makami mai suna Emmanuel Thomas Oryiman.
An samu wanda ake zargin ɗauke da bindiga guda ɗaya da harsashi guda biyu masu kaurin 9mm.
Sojoji sun sheƙe ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriƴa sun samu galaba kan ƴan bindiga bayan sun yi artabu da su a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Sojojin sun hallaka ƴan bindiga guda uku tare da ƙwato shanun da suka sace a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng