Tinubu Ya Gamu da Sabuwar Adawa Mai Zafi daga Arewa kan Kudurin Gyaran Haraji

Tinubu Ya Gamu da Sabuwar Adawa Mai Zafi daga Arewa kan Kudurin Gyaran Haraji

  • Kungiyar matasa Arewa a Taraba ta ce sabuwar dokar haraji da rufe iyakoki sun fi bai wa yankin Kudu fifiko kan Arewa
  • Kungiyar ta yi zargin cewa tsarin haraji zai rage damar Arewa wajen raya yankin da samar da aiyuka da inganta rayuwar al’umma
  • Matasan sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da ya yi adalci wajen rabon arziki, tare da kare cigaban yankin Arewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - Kungiyar hadin kan matasan Arewa reshen jihar Taraba ta ce kudirin gyaran haraji yana goyon bayan cigaban Kudu fiye da Arewa.

Matasa sun koka kan matsananciyar wahalar tattalin arziki a kasar, inda suka ce wannan dokar tana da tasiri mai muni ga Arewa.

Matasan Arewa sun yi magana kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu
Matasan Arewa sun nuna adawa a kudurorin gyaran haraji na Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Manufofin Tinubu 3 da ke dagula Arewa

Kara karanta wannan

'Arewa na fushi da kai': an gargadi Tinubu ya gyara tafiyarsa, yankin na neman mafita

Baya ga kudirin dokar haraji, kungiyar ta kuma yi tir da rufe iyakokin kasa, suna zargin an fi bai wa yankin Kudu fifiko da wannan doka, inji rahoton Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taron manema labarai a Jalingo, mai magana da yawun kungiyar, Idris Ayuba, ya ce wasu manufofin gwamnatin Bola Tinubu suna kara dagula yanayin Arewa.

Kungiyar ta ambaci cire tallafin mai, rufe iyakokin kasa, da sabuwar dokar haraji a matsayin wasu daga cikin matsalolin da Arewa ke fuskanta.

"Kudu ke amfana da manufofin Tinubu" - Ayuba

Idris Ayuba ya ce cire tallafin mai ba alama ce ta ci gaba ba, amma yana rage amfani da makamashi wanda ke jawo koma bayan tattalin arziki.

Dangane da rufe iyakoki, ya ce an rage cinikin kasuwanci da ke tsakanin kasashe, wanda hakan ya kara talauci da rashin ayyukan yi a Arewa.

Ya kara da cewa wannan manufofin suna kara wa yankin Kudu damar karuwar arziki, suna raba ayyukan tattalin arziki zuwa garesu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ce malamai da dattawan Arewa na goyon bayan kudirin harajin Tinubu

Matasa sun ba Tinubu shawarar mafita

Kungiyar ta yi zargin cewa tsarin rabon kudin shiga na dokar haraji yana sanya Arewa cikin rashin daidaito wajen samun damar raya yankin.

Kungiyar ta ce rashin kammala manyan ayyukan gwamnatin tarayya kamar Mambilla da hanyar Jalingo-Numan yana ci gaba da haifar da gibin cigaban Arewa.

Matasan sun bukaci gwamnati da ta yi la’akari da tasirin manufofinta kan Arewa tare da tabbatar da daidaito wajen raba arziki da inganta tattalin arzikin kasa.

Hanyar da talaka zai amfana da gyaran haraji

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta tabbatarwa 'yan Najeriya cewa za su amfana da kudurorin gyaran haraji idan majalisa ta amince da su.

Gwamnatin ta ce an cirewa talaka biyan haraji a wasu fannoni da dama ciki har da kayan abinci, kiwon lafiya, da kuma rage haraji kan kananun masana'antu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.