Yadda Mai Magana da Yawun Gwamna Abba Ya Tsira daga Kamun 'Yan Sanda
- Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda yake magana da yawun bakin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan yunƙurin cafke shi
- Mai magana da yawun bakin gwamnan na Kano ya bayyana cewa ya fake a gidan gwamnatin jihar domin ka da ƴan sanda su kama shi
- Sanusi Bature ya nuna cewa a yanzu ya samu umarnin kotu wanda ya hana ƴan sanda su cafke shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya bayyana cewa an yi masa katangar ƙarfe domin ya bijirewa kamun ƴan sanda.
Sanusi Bature ya bayyana yadda ya fake a gidan gwamnatin jihar Kano na tsawon kwanaki biyar domin gudun kada ƴan sanda su kama shi.

Source: UGC
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron 'PR Nigeria Young Communication Fellowship' a birnin Kano, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An so cafke hadimin Gwamna Abba
Mai magana da yawun gwamnan ya ce aƙalla jami’ai 40 daga tawagar Sufeto Janar na ƴan sanda ne, aka tura Kano domin kama shi kimanin kwanaki shida da suka gabata, rahoton DailyPost ya tabbatar.
Ya ce ya ci gaba da zama a gidan gwamnati ne, saboda kariyar da tsarin mulki ya ba shi wanda ya hana a kama kowa a cikin harabar sai da izinin gwamna.
Sanusi Bature ya bayyana cewa ya samu umarnin kotu da ya hana ƴan sanda kama shi, wanda hakan ne dalilin da ya sa ya halarci taron, ya kuma ƙara da cewa ya zama tilas ya halarci taron.
Sanusi Bature ya samu kariya
Ya kuma jaddada cewa, an kuma ba shi kariya daga kama shi.
"Akwai wannan ƙorafi a kaina wanda babu wanda yake kula da shi sai shi kansa Sufeto Janar na ƴan sanda. Ya tura tawagar jami'ai 40 zuwa Kano tun ranar Lahadi da umarnin kama ni."
"Domin haka, na fito ne saboda abubuwa guda uku kawai, na farko ba na tunanin ya kamata na rasa wannan taron ko da za a kama ni."
"Batu na biyu shi ne na samu umarnin kotu wanda ba a ba ƴan sanda ba amma tuni ya fara yaɗuwa. Domin haka, na tabbata tabbas sun gani."
"Na uku, na fito cikin ƙwarin gwiwa domin ina da ƙarfin da zan bijirewa kamu idan hakan ta faru."
- Sanusi Bature Dawakin Tofa
Gwamna Abba ya runtuma kora
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi tankaɗe da rairaya a majalisar zartaswar gwamnatinsa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallami wasu daga cikin kwamishinoninsa tare da korar sakataren gwamnatin jihar, Dr. Abdullahi Baffa Bichi.
Asali: Legit.ng

