Atiku Ya Jajantawa Ɗansa kan Babban Rashin da Ya Yi, Ya ba Shi Hakuri

Atiku Ya Jajantawa Ɗansa kan Babban Rashin da Ya Yi, Ya ba Shi Hakuri

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jajantawa dansa, Adamu Atiku kan rashin da ya yi
  • Atiku ya yi addu'a domin neman Ubangiji ya gafartawa marigayin ya kuma ba dan nasa da iyalansa hakuri
  • Hakan ya biyo bayan mutuwar daya daga cikin hadiman Adamu Atiku a bangaren sadarwa, Musty Jada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Yaron Atiku Abubakar ya yi rashin hadiminsa a bangaren sadarwa a yau Asabar 14 ga watan Disambar 2024.

Atiku ya tura sakon ta'azziya ga dan nasa da kuma iyalan marigayin mai suna Musty Jada.

Dan Atiku ya yi rashin hadiminsa na musamman
Atiku Abubakar ya tura sakon jaje ga dansa bayan rashin hadiminsa da ya yi. Hoto: @Atiku, @AdamuAtikuA.
Asali: Twitter

Adamu Atiku ya yi rashin hadiminsa

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X a daren yau Asabar 14 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya jero manyan kasa da suka halarci auren 'ya 'yansa, ya yi musu godiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan sanar da mutuwar matashin da Adamu Atiku ya yi a shafin X inda yake nuna alhini.

A cikin sanarwar, Adamu Atiku ya ce ya kadu da samun labarin rasuwar hadiminsa kuma dan a mutunsa, Musty Jada.

Adamu ya ce Jada ya wuce ma'aikaci a wurinsa sai dai aboki kuma dan uwa wanda zai yi kewar rashinsa.

Daga karshe, ya jajantawa iyalan marigayin inda ya yi masa addu'ar Allah ya sanya shi gidan aljannar Firdausi.

Atiku ya tura sakon ta'azziya ga dansa

Da yake jajantawa dan nasa da ya yi rashi, Atiku ya yi masa addu'ar samun rahama da kuma ba iyalansa hakuri.

"Kowace mutuwa tana rage al'ummarmu, ina mika ta'aziyyata kan rasuwar hadiminka a bangaren kafafen watsa labarai, Musty Jada."
"Allah ya ba ka da iyalansa da abokansa hakurin jure wannan babban rashi."
"Ina roƙon Allah Madaukakin Sarki ya yi masa rahama kuma ya sa ya huta."

Kara karanta wannan

'Ya yi kokari a mulkinsa': Basarake ya fadi dalilin kai wa Buhari ziyara a gidansa

Atiku Abubakar

Atiku ya soki yan sanda kan cin zarafi

Mun ba ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda 'yan sanda ke wuce gona da iri.

Atiku ya bayyana haka ne a martaninsa ga kama wani mai fafutuka da nuna adawa ga wasu daga cikin manufofin gwamnati.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya shawarci 'yan sanda su gaggauta sakin Dele Farotimi da ke ofishinsu a tsare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.