Malamin Musulunci Ya Roki Afuwar Al'umma kan Kiran Sanusi II da Tsohon Sarki

Malamin Musulunci Ya Roki Afuwar Al'umma kan Kiran Sanusi II da Tsohon Sarki

  • Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya nemi afuwar al'umma musamman masoya Sarki Muhammadu Sanusi II
  • Sheikh Assadussunnah ya roki yafiya bayan kiran Sanusi II da tsohon sarki yayin yi masa nasiha kan kalamansa
  • Hakan ya biyo bayan jan hankalin Sarkin kan furta cewa idan mazaje suka mari matansu su rama ba tare da bata lokaci ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya ba al'umma hakuri.

Shehin malamin ya ce ya yi nasiha ga Sarki Muhammadu Sanusi II amma bai san abin zai jawo ce-ce-ku-ce ba.

Shehin malami ya roki gafara kan kiran Sanusi II tsohon sarki
Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya nemi afuwa kan kiran Sarki Sanusi II da sunan tsohon sarki. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah.
Asali: Facebook

Sheikh Assadussunnah ya ba Sanusi II shawara

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Na fasa': Gwamna ya turje kan sabon albashin N80,000, ya fadi sharuda ga NLC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan malamin ya yi nasiha kan kalaman Sarki Sanusi II da ke cewa mata su rama idan mazajensu suka mare su.

A cikin nasihar, malamin ya soki Sarkin inda ya ce bai kamata wannan magana ta fito daga gare shi ba a matsayinsa na shugaba.

Sheikh Assadussunnah ya ce ya yi amfani da tsohon sarki wanda hakan ya batawa wasu rai inda yake ba su hakuri kan furucin.

Sheikh Assadussunnah bai sauka kan nasiharsa ba

Sai dai malamin ya kara jaddada cewa nasihar da ya yi ba zai sauka a kanta ba saboda rashin dacewar maganar Sarkin.

"Na yi nasiha ga wani shugaba, kafofin yada labarai sun ruwaito cewa yana yiwa yarsa huduba cewa idan mijinta ya mare ta ta rama."
"Ni ban sani ba na manta sai na ce tsohon Sarki, ashe akwai mutanen da kalmar tsohon sarki ta bata musu rai, ni na manta wallahi."

Kara karanta wannan

'Ba ku da hankali ne': Akpabio ga masu fada da Ministan Tinubu, ya jero dalilansa

"Saboda haka don Allah su yi hakuri da wannan kalma ta tsohon sarki tun da ba ta yi musu dadi ba."

- Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah

Malamin ya ce ya kamata ya yi amfani da kalmar daya daga cikin sarakuna inda ya sake ba su hakuri kan furucinsa.

Sai dai Assadussunnah ya ce nasihar da ya yi tana nan bai kamata a matsayinsa na shugaban ya fadi haka ba.

Sanusi II ya tsawatar kan dukan mata

Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya koka kan yadda ake samun karuwar kararrakin cin zarafi a kotunan Najeriya.

Sanusi II ya bayyana cewa masarautarsa ba za ta lamunci duk wani basarake da ke lakadawa matarsa duka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.