‘Na Fasa’: Gwamna Ya Turje kan Sabon Albashin N80,000, Ya Fadi Sharuda ga NLC
- Mako guda bayan sanya a hannu a yarjejeniya da NLC, Gwamna Umo Eno ya janye jikinsa kan sabon albashi a Akwa Ibom
- Gwamna Eno ya ce dole sai ya kammala tantance ma'aikatan jiharsa ya san yawansu kafin fara biya
- Ya zargi akwai ma'aikata da dama da ba su zuwa aiki da aka ce da yawa sun bar kasar domin neman rayuwa mai kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya janye kansa daga yarjejejniyar da ya yi da kungiyar NLC kan albashi.
Gwamna Eno ya fasa yarjejeniyar bayan mako guda da amincewa da ita kan fara biyan sabon albashin N80,000 a jihar.
Gwmana ya fadi sharadin fara biyan albashi
Premium Times ta ce gwamnan ya amince tun farko zai fara biyan albashin a watan Disamba kafin sauya ra'ayinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Eno ya dole sai ya kammala bincike kan hakikanin yawan ma'aikatan jihar kafin ya fara biyan albashin.
Ya zargi akwai ma'aikatan bogi da kuma wadanda sun bar kasar tuntuni amma sunayensu na cikin jerin ma'aikata.
Sai dai duk da haka gwamnan ya yi alkawarin biyan albashin watanni 13 ga ma'aikata saboda bata musu lokaci kan binciken.
'Babu mai tilasta ni biya' - Gwamna Eno
"Mun yi ganawa mai zafi da kungiyar NLC kan biyan albashin daga Nuwamba, amma na ce ya kamata mu tantance ma'aikata."
"Ko yau aka gama tantance ma'aikata zan fara biyan sabon albashi tun daga Nuwamba wanda na yi alkawarin biyan watanni 13 wanda mun gama lissafawa.'
"Babu wanda zai tilasta ni yin haka, dole na san yawan ma'aikata da ke aiki, idan NLC ta bani a yau, ni kuma gobe zan fara biya."
- Umo Eno
Gwamna sun gana da NLC, zai biya N80,000
Kun ji cewa Ƙungiyar kwadago rashen jihar Akwa Ibom ta fasa yajin aiki bayan Gwamna Umo Eno ya amince da N80,000 a mafi karancin albashi.
Shugaban NLC, Sunny James ya ce gwamnan ya kuma kara N32,000 a kuɗin da ake ba ma'aikatan da suka yi ritaya duk wata.
Asali: Legit.ng