Kudin da Gwamnatin Tarayya, Gwamnoni Suka Raba Ya Karu da Naira Biliyan 300 a FAAC

Kudin da Gwamnatin Tarayya, Gwamnoni Suka Raba Ya Karu da Naira Biliyan 300 a FAAC

  • An raba makudan kudi da aka yi zaman FAAC domin kuwa N1.7tr ya shigo cikin asusun gwamnatin Najeriya
  • Duk da abin da aka samu daga VAT ya ragu, gwamnonin jihohi sun tashi da kusan N300bn a Nuwamban 2024
  • An ba jihohin da suke da arzikin mai karin N190bn daga cikin kudin da aka samu a watan da ya gabata

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kwamitin FAAC da ke da alhakin rabon kudin da aka samu a tarayya ya raba N1.72tr tsakanin bangarorin gwamnati.

Gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi da kananan hukumomi sun tashi da N1.72tr da aka yi zaman kaso na watan Nuwamba.

FAAC.
Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni sun samu N1.7tr a FAAC Hoto: @FinMinNigeria
Asali: Twitter

FAAC: N3.14tr ya shigowa Gwamnatin tarayya

Idan aka kamanta da abin da aka samu a Oktoban 2024, tashar NTA ta kasa ta ce an samu karin har N310bn a kason FAAC.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, CBN ya yi magana kan daina amfani da tsofaffin kuɗi a ƙarshen 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani jawabi da ya fito daga ma’aikatar tattalin arziki a X, an fahimci N3.14tr ya shigo cikin asusun tarayya a karshen Nuwamba.

Daga cikin fiye da N3tr da aka samu, jawabin ya ce abin da aka iya rabawa bangarorin gwamnatin Najeriya a watan shi ne N1.7tr.

Yadda aka rabawa gwamnatoci kudi a Nuwamba

The Cable ta rahoto cewa ministan tattalin arziki watau Wale Edun ya jagoranci zaman na FAAC kamar yadda aka saba a al’ada.

Rahoton ya ce kudin da aka samu sun fito ne daga haraji irinsu VAT da EMTL, kuma a karshe gwamnatin tarayya ta tashi da N581bn.

Gwamnonin jihohi sun samu N549.79bn sai aka ba kananan hukumomin N402.55bn.

Jihohin da suke da danyen mai sun samu karin N193.29bn a matsayin 13% na arzikinsu kamar yadda sanarwar da aka fitar ta nuna.

VAT ya ragu a watan Nuwamba

An fahimci cewa VAT da aka samu a Nuwamba ya ragu ne domin N628.9bn aka tatsa. Daga ciki ne aka rabawa gwamnatocin kasar.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunno kai a tsakanin gwamnonin jihohi 36 kan kudirin harajin Tinubu

Gwamnatin tarayya ta karbi N87bn, gwamnoni kuma sun samu N292.8bn, sai shugabannin kananan hukumomi suka samu N204bn.

Gwamnatin tarayya da Facebook suna kotu

Gwamnatin tarayya ta zargi Facebook da sabawa ka'idoji don haka aka ci ta tarar N60bn kamar yadda labari ya gabata kafin yanzu.

Alkali ya bukaci hukumar ARCON ta bar magaar wannan haraji bayan Facebook ya dauko hayar wani lauya wanda ya yi karatu a waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng