Sanata Barau Ya Jero Manyan Kasa da Suka Halarci Auren 'Ya 'Yansa, Ya Yi Musu Godiya
- Sanata Barau Jibrin ya gode wa Allah (SWT) kan nasarar daurin auren 'ya'yansa biyu, Jibrin Barau I. Jibrin da Aisha Barau
- Manyan mutane daga fannonin rayuwa daban-daban sun halarci taron auren da ya gudana a masallacin Ƙasa na Abuja
- Biyo bayan kammala hidimar bikin, mataimakin shugaban majalisar dattawan ya mika godiya ga dimbim wadanda suka halarci daurin auren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya mika godiya mai yawa ga Allah (SWT) kan nasarar da aka samu a daurin auren 'ya'yansa biyu.
Limamin masallacin kasa na Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya jagoranci daurin auren kuma bikin ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan da ma ƙetare.
Sanata Barau Jibrin ya wallafa sakon fatan alheri da godiya ga wandanda suka halarci auren a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau ya godewa Tinubu da manyan baƙi
Sanata Barau Jibrin ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kasance wakili yayin auren.
Ya kuma godewa gwamnoni, sanatoci, ministoci, ‘yan majalisar wakilai, 'yan kasuwa, sarakuna, da malaman addini inda ya ce kasancewarsu a wurin ya ƙara wa bikin armashi.
Barau Jibrin ya ce goyon bayan da ya samu alama ce ta haɗin kai da soyayya da ke tsakanin ‘yan ƙasa.
Barau ya yi godiya ga mutanen Kano
Sanatan ya yi godiya ga shugaban APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje da sauran 'yan jam'iyyar, musamman jama’ar mazabar Kano ta Arewa da mutanen Kano baki ɗaya.
Mataimakin majalisar dattawan ya ce goyon bayansu a lokacin bikin abin alfahari ne ga shi kansa da iyalinsa.
Haka zalika, ya mika godiya ga dukkan hadiman shugaban ƙasa da suka halarci auren, tare da fatan alheri ga waɗanda suka zo daga wurare masu nisa.
Fatan alheri ga amarya da ango
Sanata Barau Jibrin ya yi addu’ar Allah (SWT) ya albarkaci zaman auren 'ya'yansa, ya cika rayuwarsu da soyayya, salama, da farin ciki mara yankewa.
Ya kuma yi godiya ga duk waɗanda suka halarci bikin ko suka taya su murna a zuciya, yana cewa Allah ya saka da alheri.
An daura auren 'ya'yan Barau da sarkin Bichi
A wani rahoton, kun ji cewa jiga jigan 'yan siyasa da dattawa sun halarci bikin daurin auren 'ya'yan Sanata Barau Jibrin.
Rahotanni sun nuna cewa an daura auren ne tsakanin iyalan Barau da mai martaba Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero a masallacin kasa na Abuja.
Asali: Legit.ng