Kotu Ta Dakile Ganduje, Ta Ba da Umarni ga Jami'an Tsaro kan cafke Kakakin Abba Kabir
- Babbar kotun jihar Kano ta dakile jami'an tsaro kan kokarin kama hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren sadarwa
- Kotun ta umarci dukan jami'an tsaro su guji shiga hakkin Sanusi Bature Dawakin-Tofa kan zargin da ake yi masa
- Hakan na zuwa ne bayan korafin Dr. Abdullahi Ganduje kan zargin Dawakin-Tofa da kisa tsige shi a gundumarsa watannin baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Babbar Kotun jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da hukumomin tsaro cafke hadimin Gwamna Abba Kabir.
Ana zargin Sanusi Bature Dawakin-Tofa da shirya tsige tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a gundumarsa.
Kotu ta haramta kama hadimin Abba Kabir
Daily Nigerian ta ce hakan ya biyo bayan korafin da shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje ya shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya zargi Dawakin-Tofa da jagorantar tsige shi daga jam’iyyar APC a matakin mazabu watanni shida da suka wuce.
Kotun ta bayar da umarnin ne domin kare wanda ake zargin daga abin da tawagar lauyoyinsa suka bayyana a matsayin 'cin zarafi da muzgunawa'.
A cewar rahotanni, umarnin kotun ya haramta duk wani mataki da zai keta hakkokin Dawakin-Tofa na ‘yancin kai da daraja da walwalarsa.
Zargin Ganduje kan hadimin Abba Kabir
Rigimar ta bullo ne bayan zargin da Ganduje ya yi na wani makarkashiya da ya ce Dawakin-Tofa suka fito daga karamar hukuma daya da gwamnatin NNPP ta Kano suka yi.
Bayan korafin Ganduje, IGP ya gayyaci Dawakin-Tofa zuwa Abuja da shugabannin mazabar APC na Ganduje kan zargin makarkashiya da ayyukan da ka iya kawo rikici.
Lauyan Dawakin Tofa, Barista Haruna Musa Muhammad ya kalubalanci gayyatar yana mai cewa wannan wata dabara ce ta bata masa suna da kuma kawo cikas ga ayyukansa.
Daga bisani, an dage cigaba da shari'ar har zuwa ranar 22 ga Janairun 2025 mai zuwa.
Kotu ta zauna kan tuhumar Ganduje da almundahana
Kun ji cewa Babbar kotun Kano ta dage shari'ar Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutum bakwai kan zargin cin hanci da karkatar da kudade.
Lauyoyin wadanda ake tuhuma sun bukaci karin lokaci don gyara takardunsu, yayin da kotu ta dage sauraron karar zuwa 2025.
Asali: Legit.ng