Bola Tinubu Ya Tausaya, Ya Saka Tallafin Kashi 50% a Kayan Noma
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri na tallafin noman alkama domin rage dogaro da shigo da abinci daga ƙetare
- Rahotanni sun tabbatar da cewa shirin tallafin zai shafi manoma 280,000 a jihohi 16 da ke noman alkama a Najeriya.
- A karkashin shirin, manoma za su samu tallafin na kashi 25% kan iri da kashi 50% kan takin zamani domin bunkasa noma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wani shiri mai muhimmanci domin ƙarfafa noman alkama a Najeriya.
Gwamnatin Bola tinubu ta bayyana cewa an kawo tallafin ne domin inganta samar da abinci da kuma rage dogaro da alkamar da ake shigowa da ita daga ƙetare.
Ma'aikatar yada labarai ta wallafa cewa ministan kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana lamarin a Abuja yayin da yake tattaunawa da manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin tallafawa manoman Najeriya 280,000
A cewar daraktan shirin, Ishaku Buba za a tallafawa manoma 280,000 waɗanda suka haɗa da ƙananan manoma da matsakaita a jihohi 16.
Haka zalika, za a ba da tallafi mai tsoka ga manoman, inda aka tanadi tallafin kashi 25% kan irin alkama da kuma kashi 50% kan takin zamani dominn rage farashi ga masu noman.
Saboda yanayin ƙasa da kuma himmar gwamnatin jihar Jigawa wajen ƙarfafa noman alkama, za su sami ƙarin kayan aikin gona fiye da sauran jihohi.
An kafa cibiyoyin rabon tallafin noma
Shirin ya kafa cibiyoyin rabon tallafi guda 409, daga cikinsu 281 suna aiki a halin yanzu, wanda ake sa ran manoma 68,389 za su ci gajiya.
Ana sa ran za a kammala rabon kayan aiki nan da ƙarshen watan Disamba, domin hakan ya dace da lokacin noman alkama a Najeriya.
Don tabbatar da tsaro a lokacin rabon kayan, an tanadi jami’an tsaro daga ‘yan sanda, DSS, da kuma NSCDC a wuraren rabon kayan aiki.
Tallafin zai tabbatar da isasshen abinci a ƙasa
Ministan Kuɗi, Wale Edun ya ce shirin zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin karkara da rage dogaro da shigo da alkama daga ƙetare.
The Nation ta rahoto cewa Wale Edun ya ce shirin zai kawo gagarumin ci gaba wajen samar da abinci mai yawa da kuma ƙara samun walwala a tsakanin al’umma.
Tinubu zai raba tallafin $134m ga manoma
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta cigaba da shirin tallafawa manoma domin wadatar da Najeriya abinci.
Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka yayin kaddamar da shirin noman rani da za a yi a zangon 2024/2025.
Asali: Legit.ng