Yadda Miji Ya Kulle Matarsa a Daki Ya Cinnawa Kansu Wuta da Fetur

Yadda Miji Ya Kulle Matarsa a Daki Ya Cinnawa Kansu Wuta da Fetur

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Ondo sun nuna cewa wani mai gida ya ƙone kansa tare da matarsa bayan wata matsala ta aure
  • An ruwaito cewa mijin ya mutu nan take, yayin da matarsa ke asibiti tana karɓar magani rai a hannun Allah
  • Karin rahotanni sun nuna cewa mijin ya yi wannan aika-aikar ne saboda matarsa ta ƙi dawo wa gidan aurensu bayan sun samu matsala

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Wani mutum da ba a bayyana sunansa ba ya ƙone kansa da matarsa a unguwar Ijoka, Akure ta Jihar Ondo a ranar Juma’a.

Mijin ya mutu a sanadiyyar wutar yayin da matarsa ta tsira da raunuka masu tsanani kuma tana karɓar magani a asibiti.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojoji suka hallaka 'yan ta'adda 181 yayin artabu

Jihar Ondo
Miji ya kona matarsa a Ondo. Hoto: Legit
Asali: Original

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin ta shafinta na X, inda ta bayyana cewa miji ya ɗauki wannan matakin ne bayan matarsa ta ƙi dawo wa gidan aurensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mata da miji suka kone

Bayan wasu ma’aurata sun shafe shekaru 10 suna zaune tare da haihuwar ‘ya’ya biyu, an samu wata matsala ta haifar da rabuwarsu.

Wani jami’in ‘yan sanda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce mijin ya dade yana roƙon matarsa ta dawo, amma ta ƙi amincewa.

"A ranar da abin ya faru, ya gayyaci matar zuwa gidansa domin ɗaukar wani abu. Bayan ta iso, ya fara roƙonta su sulhunta, amma ta ƙi amincewa.
Wannan ne ya sa ya kulle ƙofar daga baya, ya ɗauki fetur ya zuba, sannan ya banka wuta,"

- Jami'in dan sanda

Miji ya mutu, mata na kwance a asibiti

Kara karanta wannan

An kama masu taimakon 'yan bindiga da kayan sojoji da 'yan sanda

Punch ta wallafa cewa rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa mijin ya mutu nan take a wutar, yayin da matarsa ke fama da raunuka masu tsanani.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Funmilayo Odunlami ta ce matar tana karɓar magani a wani asibiti, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Mata da miji sun rasu a Kano

A wani rahoton, kun ji mata da miji sun rasu sakamakon ibtila'in gobara da ya faru ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da mutuwar ma'auratan, ta ce sun mutu ne sakamakon raunuka da shakar hayaƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng