Shugaban Majalisa Ya Fadi Ainihin Dalilin Tinubu Na ba Wike Mukamin Minista

Shugaban Majalisa Ya Fadi Ainihin Dalilin Tinubu Na ba Wike Mukamin Minista

  • Shugaban majalisr dattawan Najeriya ya yi ƙarin haske kan dalilin mai girma Bola Tinubu na Nyesom Wike muƙamin minista
  • Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa Tinubu ya ba Wike minista ne saboda rawar da ya taka a muƙaman da ya taɓa riƙewa a baya
  • Akpabio ya kuma yabi Wike kan yadda ya gyara babban birnin tarayya Abuja tun bayan zamansa minista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi magana kan zaman Nyesom Wike minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Sanata Godswill Akpabio ya ce irin rawar da tsohon gwamnan ya taka a muƙaman da ya riƙe a baya, ta sanya Tinubu ya ba shi minista.

Akpabio ya yabi Nyesom Wike
Akpabio ya fadi dalilin Tinubu na ba Wike mukamin minista Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani littafi, domin murnar cikar Wike shekara 57, a birnin Port Harcourt na jihar Rivers, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Tinubu ya naɗa Wike minista?

A cewar Akpabio, Shugaba Tinubu ya naɗa Wike ne saboda irin rawar da ya taka a matsayin shugaban ƙaramar hukuma, shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Rivers, minista da gwamna na wa'adi biyu, rahoton The Nation ya tabbatar.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana Wike a matsayin mai aiki tuƙuru wanda ya ke bayar da gudunmawa a duk ofishin da ya samu kansa.

"Bari in fada maka dalilin da yasa Shugaba Tinubu ya zaɓe ka domin shiga majalisar zartaswa (FEC) duk da kasancewarka ɗan siyasan adawa."
"Ayyukanka, a matsayinka na shugaban ƙaramar hukuma, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Rivers, minista, da gwamna na wa’adi biyu ya sa ka samu wannan muƙamin."
"Ka sanya mu alfahari a matsayinka na ministan Abuja. Ka mayar da Abuja kyakkyawan birnin da ya dace da zama babban birnin ƙasa."
"Kai jami'in gwamnati ne mai himma wanda ba shi da wasa akan kowane aiki da aka bayar. Cikin ƙasa da shekara biyu ka mayar da Abuja babban wurin gine-gine."

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya yabi Tinubu ana batun kudirin haraji

- Sanata Godswill Akpabio

Majalisar dattawa za ta gayyaci Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisr dattawan Najeriya ta kafa wani kwamitin bincike nan rushe gine-ginen da ake yi a birnin tarayya Abuja.

Kwamitin binciken zai gayyaci ministan Abuja, Nyesom Wike, domin yin.bayani kan dalilin da ya sanya ake rushewa mutane gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng