Tarin 'Yan Acaba Sun Kai Hari Caji Ofis, Sun yi wa 'Yan Sanda Rubdugu

Tarin 'Yan Acaba Sun Kai Hari Caji Ofis, Sun yi wa 'Yan Sanda Rubdugu

  • Ana zargin 'yan acaba sun kai hari kan ofishin 'yan sanda a Oka-Akoko a jihar Ondo sakamakon rashin jituwa da aka samu
  • Wata majiya ta bayyana cewa 'yan acaban sun zargi 'yan sandan da boye direban mota da ya lalata babur din ɗaya daga cikin abokan aikinsu
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan acaban sun ji wa jami'an 'yan sanda rauni tare da kwace wayar hannu ta wani babban jami'in 'yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar ondo - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu 'yan acaba sun kai hari kan ofishin 'yan sanda a Oka-Akoko, karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma a Jihar Ondo.

An kai harin ne bayan wata hatsaniya da suka ce direban mota ya haddasa, inda ya lalata babur din ɗaya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Yan sanda, sarakuna da mutanen gari sun hadu domin murkushe 'yan daba a Kano

Acaba
'Yan acaba sun kai hari caji ofis. Hoto: Kola Sulaimon (An yi amfani da hoton ne domin buga misali)
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa harin ya yi sanadin raunin wasu jami'an 'yan sanda, inda aka kuma kwace wata wayar hannu ta wani babban jami'in ofishin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikici tsakanin 'yan acaba da 'yan sanda

'Yan acaba sun kai farmaki kan ofishin 'yan sanda a Oka-Akoko, suna zargin jami'an da boye direban mota da ya lalata din babur ɗaya daga cikin abokan aikinsu.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wata hatsaniya da ta faru a kan titin Epinmi, inda direban mota ya buge wani ɗan achaba.

"Mun samu kiran gaggawa kuma nan take muka garzaya wajen, muna zuwa muka mika masu rauni asibiti. Ba da jimawa ba sai muka ga mutane da dama sun taho suna neman direban,"

- 'Yan sanda

'Yan acaba sun kai hari caji ofis

Jami’in ya ce 'yan acaban da suka kai hari kan ofishin sun kai kimanin mutum 100, inda suka ji wa jami’an rauni kuma suka kwace wata waya ta babban jami’i.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi fitar dango, sun kora mazauna kauyen Sakkwato cikin daji

Ya ce jami’an sun yi ƙoƙarin shawo kan lamarin domin guje wa barna, amma masu harin sun fi ƙarfin su saboda yawansu.

Haka kuma, wani jami’in ya tabbatar da cewa 'yan sanda sun kama mutane biyu daga cikin waɗanda suka kai harin.

Sarkin Oka ya yi tir da harin 'yan acaba

Sarkin garin Oka, Oba Yusuf Adebori Adeleye, ya yi tir da harin da 'yan acaban suka kai kan ofishin 'yan sanda.

Ya ce irin wannan hali ba zai haifar da zaman lafiya a al’umma ba, yana mai kira ga mutane da su zauna lafiya tare da mutunta dokokin ƙasa.

Sojoji sun dakile hari a kasuwa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar Sojojin Najeriya ta dakile wani hari da ‘yan bindiga suka shirya kaiwa a Kudancin jihar Taraba.

Legit ta ruwaito cewa sojoji sun kama wasu mutane biyu, Terry Waapara da Tobaya Tekura, dauke da bindigogin AK-47 da suka nufi kai hari kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng