Sojoji Sun Durfafi 'Yan Ta'addan Lakurawa, Sun Samu Tarin Nasarori

Sojoji Sun Durfafi 'Yan Ta'addan Lakurawa, Sun Samu Tarin Nasarori

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasarori a kan ƴan ta'addan Lakurawa a jihohin Kebbi da Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Rundunar sojojin ta musamman ta yi nasarar ragargazar ƴan ta'ddan na Lakurawa a jihohin guda biyu da ke Arewacin Najeriya
  • Sojojin sun yi nasarar lalata sansanonin ƴan ta'addan guda 22 yayin da suke ci gaba da ƙoƙarin ganin sun fatattake su daga Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Rundunar sojojin Najeriya ta musamman ta yi nasarar fatattakar ƴan ta'addan Lakurawa da dama.

Rundunar sojojin ta kuma lalata sansanoni kusan 22 na ƴan ta'addan a jihohin Sokoto da Kebbi.

Sojoji sun ragargaji 'yan Lakurawa
Sojoji sun lalata sansanonin 'yan ta'addan Lakurawa Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Babban kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele, shine ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma'a a Sokoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'addan Lakurawa

Kara karanta wannan

Lakurawa sun shiga uku: Hafsan tsaro ya tura dakaru na musamman, ya fadi shirinsu

Ya bayyana hakan ne ta bakin muƙaddashin babban kwamandan runduna ta 8, ta sojojin Najeriya dake Sokoto, Birgediya Janar Ibikunle Ajose.

Soyele ya ce, babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa ne ya tura rundunar ta musamman domin gudanar da aikin.

Ya ƙara da cewa an samu nasarorin ne ta hanyar sababbin hare-hare da aka kai kan ƴan ta'addan Lakurawa, wanda ya kai ga lalata sansanoninsu.

Ya kuma umarci sojojin da su tabbatar da lalata ƴan ƙungiyar ta Lakurawa, sannan ya buƙace su da su bi ƙa’idojin aiki tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Soyele ya ƙara da cewa wannan aiki na musamman, ana yinsa ne domin tabbatar da ganin an kawar da ƴan ƙungiyar Lakurawa gaba ɗaya a jihohin Sokoto da Kebbi.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu gudanar da ayyukan yaƙi da ta'addanci sun kashe ƴan ta'adda aƙalla 181 a cikin makon da ya gabata.

Dakarun sojojin sun cafke masu laifi 203, da suka haɗa da ɓarayin mai guda 50, tare da ceto mutane 161 da aka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng