Lakurawa Sun Shiga Uku: Hafsan Tsaro Ya Tura Dakaru na Musamman, Ya Fadi Shirinsu
- Gwamnatin Bola Tinubu ta himmatu wurin tabbatar da samun ingantaccen tsaro a Najeriya musamman a Arewacin kasar
- Rundunar sojojin ta tura dakaru na musamman domin kawo karshen yan kungiyar Lakurawa da suka addabi jihohin Sokoto da Kebbi
- Sojojin da za a tura za su fi ba da karfi ne a yankunan da Lakurawa suka fi addabar mutane da kuma maboyarsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa ya shirya kawo karshen yan kungiyar Lakurawa gaba daya.
Janar Musa ya tura wata runduna ta musamman domin yakar yan kungiyar a jihohin Sokoto da Kebbi.
Sojoji sun shirya yakar Lakurawa da gaske
An sanar da wannan tura rundunar a ranar Juma’a 13 ga watan Disambar 2024, kamar yadda shafin Zagazola Makama ta tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan wani bangare na kokarin kara tabbatar da nasarar da aka samu ta hanyar 'Operation Forest Sanity III' da kuma kawar da ayyukan kungiyar Lakurawa baki daya a yankin.
Babban kwamandan runduna ta 8, Birgediya-janar Ibikunle Ajose ya yi jawabi ga sojojin a Sokoto a madadin kwamandan yankin, Manjo-janar Oluyinka Soyele.
Ajose ya bukaci sojojin da su cigaba da nuna kwarewa a aikinsu tare da bin dokokin aiki yadda ya kamata yayin gudanar da shi.
Ya jaddada mahimmancin kare rayuka da dukiyoyin al’umma masu bin doka yayin gudanar da aikin.
Yankunan da dakarun za su fi ba karfi
Rahoton ya ce aikin ya mayar da hankali ne kan maboyar kungiyar da aka gano a Rumji Dutse da Gabashin Sarma da Tsauna da Bauni da Malgatawa.
Sai kuma Gargao da Tsauna da dazukan Magara da kauyukan Kaideji da Nakuru da Sama.
Sauran sun hada da Sanyinna da Kadidda da Kolo da Dancha a kananan hukumomin Illela da Tangaza da Binji.
Ta'addancin da Lakurawa ke yi a Arewa
A wani labarin, kun ji cewa hukumomin Najeriya sun tabbatar da samuwar sabuwar kungiyar yan ta'addan Lakurawa a wasu sassa na Sokoto da Kebbi.
Mazauna wuraren da yan ta'addar ke zama sun bayyana yadda suka fara muzgunawa al'umma da ta'addancin da suke yi.
Asali: Legit.ng