Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 181 tayin Artabu

Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 181 tayin Artabu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a kan ƴan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan yayin artabun da suka yi
  • Sojojin masu yaƙi da ta'addanci sun hallaka ƴan ta'adda 181 a faɗin Najeriya a cikin makon da ya gabata
  • Jami'an tsaron sun kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da cafke ɓarayin mai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Dakarun sojojin Najeriya masu gudanar da ayyukan yaƙi da ta'addanci sun kashe ƴan ta'adda aƙalla 181 a cikin makon da ya gabata.

Dakarun sojojin sun cafke masu laifi 203, da suka haɗa da ɓarayin mai guda 50, tare da ceto mutane 161 da aka yi garkuwa da su.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 181 a mako guda Hoto: Zagazola Makama
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi galaba kan 'yan bindiga, sun ceto mutanen da suka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun fatattaki ƴan ta'adda

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama, har da wani mai safarar bindigogi mai suna Mohammed Musa wanda aka fi sani da Mamman, rahoton Channels tv ya tabbatar.

"A cikin makon, sojoji sun kashe ƴan ta’adda 181 tare da kama mutane 203 da ake zargi da aikata laifuka."
"Sojojin sun kuma kama mutane 50 da suka aikata laifin satar mai tare da ceto mutane 161 da aka yi garkuwa da su."
"Bugu da kari, an kama wasu tantiran masu garkuwa da mutane da wani mai safarar bindigogi, mai suna Mohammed Musa (wanda aka fi sani da Mamman)."
"Duk ƙoƙarin da ake yi, ana yi ne domin rage ƙarfin ƴan ta'adda a duk inda suke samun mafaka."

- Manjo Janar Edward Buba

Manjo Janar Edward Buba ya kuma bayyana cewa an ƙwato ɗanyen mai wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan 728.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda a wani artabu, sun kwato makamai

Dakarun Sojoji sun yi ƙoƙari

Wani mazaunin jihar Katsina mai suna Sani Abdullahi, ya shaidawa Legit Hausa cewa dakarun sojojin sun yi ƙoƙari sosai kan nasarorin da suka samu.

"Lamarin tsaro yana ƙara inganta, muna yabawa da nasarorin da sojoji suke samu kan ƴan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan."

- Sani Abdullahi

Sojoji sun kashe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a jihar Zamfara.

Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun hallaka ƴan ta'addan ne bayan sun yi artabu da su a ƙaramar hukumar Anka ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng