Tijjani Babangida Ya Fadi Halin da Matarsa, Maryam Waziri Ke Ciki, Turawa Sun Tallafa Masa

Tijjani Babangida Ya Fadi Halin da Matarsa, Maryam Waziri Ke Ciki, Turawa Sun Tallafa Masa

  • Kngiyar kwallon kafa a kasar Netherlands ta yi hira ta musamman da tsohon dan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida
  • Babangida ya bugawa kungiyar kwallon kafa lokacin da yake kan ganiyarsa kafin yin ritaya daga buga wasanni
  • Hakan ya biyo bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi a watan Mayun 2024 da ya yi sanadin rasa dansa da kaninsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Amsterdam, Netherlands - Tsohon dan wasan Super Eagles, Tijani Babangida ya yi magana kan halin da suke ciki da iyalansa.

Fitaccen dan wasan ya bayyana mummunan tashin hankali da ya fuskanta na rasa ɗansa da ɗan uwansa a wani hatsarin mota.

Tijjani Babangida ya fadi yadda yake ji bayan rasa dansa da kaninsa
Tsohon dan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida tuno irin jarabawar da ya gamu da ita a hatsarin mota a Kaduna. Hoto: Maryam Waziri.
Asali: Facebook

Hatsarin motar da ya gigita Tijjani Babangida

Babangida ya fadi haka a cikin wani faifan bidiyo da tsohuwar ƙungiyarsa ta Ajax ta yi hira da shi na musamman da @oluwashina ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Shugaban karamar hukuma ya riga mu gidan gaskiya a hatsari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan gamuwa da mummunan hatsari mota mai ban tsoro da suka yi a jihar Kaduna.

Bayan rasa dansa da dan uwansa, hatsarin ya kuma jikkata matarsa, tsohuwar jarumar Kannywood, Maryam Waziri.

Matar ta samu munanan raunuka da suka haɗa da rasa ido ɗaya da kuma wani ɓangare na fuskarta.

Kungiyar Ajax tana tallafawa Tijjani Babangida

Kungiyar AFC Ajax tana ƙoƙarin taimakawa Babangida wajen tara kuɗi don murmurewarsa da kuma kara masa karfin guiwa.

A cikin hirar da suka yi, Babangida ya bayyana irin azabar da ya sha na rasa dansa da kaninsa yayin hatsarin motar.

“Wannan mummunan abu ne mai ban tsoro, ina tsammanin zan rayu da wannan damuwar har ƙarshen rayuwata."
"Abin yana da matuƙar wahala a manta da shi kuma a cigaba da rayuwa yayin da ka rasa duka iyalanka kwatsam.”
“Ta kasance mace mai cike da fara’a, bayan shekara ɗaya da aure, mun haifi kyakkyawan yaro dan wani saurayi da ake kira Fadeel, amma kwatsam, mun rasa shi.”

Kara karanta wannan

"Babu abin da ya same ni," Dan majalisar tarayya ya musanta labarin rasuwarsa

- Tijjani Babangida

Fatan Tijjani Babangida a rayuwarsa

Yayin da Babangida da matarsa ke cigaba da murmurewa daga wannan jarabawa, suna fatan samun kyakkyawar makoma.

“Ina so in more rayuwa mara wahala, ina fatan komai zai tafi daidai kan lamarin matata, ina fata za ta iya dawo da rayuwarta yadda ta kasance."

- Tijjani Babangida

Peter Obi ya ziyarci Tijjani Babangida

Kun ji cewa yayin da tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida ya gamu da hatsari, dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya ziyarce shi.

Obi ya kai ziyarar, ya ce ya dauki matakin ne domin jajantawa Babangida kan rashin da ya tafka a hatsarin mota.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.