Rigimar Saurata Ta Barke kan Birne Tsohon Sarki, An Zargi Masarauta da Rashin Gaskiya

Rigimar Saurata Ta Barke kan Birne Tsohon Sarki, An Zargi Masarauta da Rashin Gaskiya

  • Rigima ta barke kan shirye-shiryen birne marigayi tsohon basarake a jihar Osun saboda zargin tatsar kudi
  • Ana rigimar tsananin 'ya'yan marigayin Oba Gabriel Adekunle na Ijesa da kuma kwamitin masarauta
  • Iyalan sun zargi kwamitin masarautar da tatsarsu makudan kudi ta kowane hali domin shirin birne marigayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Dangantaka tsakanin ‘ya’yan wani marigayi basarake da kwamitin masarauta ta yi tsami a jihar Osun.

Rigimar ta barke ne kan zargin tatsarsu kudi masu yawa da masarautar Ijesa ke yi kan shirin birne mahaifinsu.

An samu hatsaniya kan zargin rashin gaskiya a batun birne tsohon sarki
Rigimar sarauta ta barke a jihar Osun kan zargin rashin gaskiya a kokarin birne tsohon sarki. Hoto: Legit.
Asali: Original

'Ya'yan sarki sun tada bore kan birne mahaifinsu

Tribune ta ce ana ta shirye-shiryen birne marigayi Owa Obokun Adimula na Ijesa, Oba Gabriel Adekunle Aromolaran cikin lumana kafin baraka ta barke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin ya barke ne kan zargin rashin gaskiya wajen sarrafa kudaden da aka bayar domin shirya jana’izar basaraken.

Kara karanta wannan

Gwamna na kuntatawa 'yan majalisu masoyan tsohon gwamna? hadiminsa ya magantu

Iyalin sun nuna rashin jin daɗinsu game da abin da suka kira “dawainiyar karya” da kwamitin suka dora musu da biyan kudade da ba su dace ba a matsayin “al’adun karya” bayan rasuwar basaraken.

Masarautar ta mayar da martani mai zafi

Sai dai a martaninsa, wani mai fada a ji a masarautar wanda shi ne Owa na Ijesa, Bola Orolugbagbe ya musanta zargin.

“Ku ce su fadi sunayen sarakunan da suka nemi su biya waɗannan kudade, shikenan."
"Ba mu da laifi, su kawo sunayen waɗannan sarakunan, sannan a wallafa su a jarida da yanar gizo, ko inda suka ga dama.”

- Bola Orolugbagbe

Dangin marigayi basaraken waɗanda suka haɗa da Aleki na Ileki-Ijesa, Onikedun na Ikedun-Ijesa sun ce an tilasta su biyan kuɗaɗe masu yawa ba da yardarsu ba.

A wata sanarwa da ‘ya’yan basaraken da sauran ‘yan uwa suka sanya hannu a kai, sun yi tir da rashin gaskiya wajen sarrafa kudaden jana’izar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

Lamidon Adamawa: Gwamna ya kassara ikon sarki

Kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Adamawa ta gabatar da kudiri game da kirkirar sababbin sarakuna zuwa matakin darajar farko.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shi ya gabatar da kudirin domin inganta shugabancin sarakunan gargajiya a jihar Adamawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.