Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Shilla Dubai, Zai Wakilci Bola Tinubu a Kasar Waje

Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Shilla Dubai, Zai Wakilci Bola Tinubu a Kasar Waje

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya fice daga kasar nan zuwa hadaddiyar daular Larabawa da yammacin Juma'a
  • Sanata Kashim Shettima zai wakilci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kaddamar da cibiyar adana man fetur da dangoginsa
  • Daga can, mataimakin shugaban zai wuce kasa mai tsarki domin sauke farali, ana sa ran dawowarsa Najeriya a ranar 20 Disamba, 2024

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Najeriya a yammacin Juma’a domin halartar taron kaddamar da ma’ajiyar mai a Dubai.

Sanata Kashim Kashim zai wakilci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a taron da ake sa ran kaddamar da cibiyar ajiyar mai mai darajar $315m.

Kashim
Kashim Shettima ya tafi Dubai Hoto: @stanleynkwocha
Asali: Twitter

A sakon da hadimin Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na X, cibiyar da za a kaddamar mallakin kamfanin Najeriya ne mai suna ‘Oriental Energy Limited.’

Kara karanta wannan

An samu matsala, Tinubu ya dakatar da gabatar da kasafin kudin 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima zai wakilci Tinubu a Dubai

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai halarci kaddamar da cibiyar adana man fetur a ranar Asabar, 14 Disamba, 2024.

Ana sa ran da zarar an kammala kaddamar da cibiyar, Kashim Shettima zai bar Dubai zuwa kasar Saudiyya, kafin ya juyo zuwa gida, Najeriya.

Daga nan, Kashim Shettima za iyi Umrah

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai ziyarci garuruwan Madinah da Makkah a ranar 16 – 17 Disamba, 2024 domin gudanar da aikin umrah.

Daga nan shugaban zai gana da shugaban bankin cigaban kasashen musulunci (IsDB) domin tattauna makomar shirinsu na habaka sarrafa kayan noma kashi na II a kasar nan.

Ana sa ran Sanata Kashim zai dawo Najeriya a ranar 20 Disamba, 2024 domin cigaba da gudanar da ayyukan kasa.

Kashim Shettima ya ziyarci Kano

A baya, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kawo ziyara Kano a dai-dai lokacin da ake dambarwar ta sauya salo, har ta kai ga girke jami'an tsaro a kofar kudu.

Kara karanta wannan

'Arewa na fushi da kai': an gargadi Tinubu ya gyara tafiyarsa, yankin na neman mafita

Sanata Kashim Shettima ya ziyarci rukunin kamfanoni da ke Challawa, ya ziyarci kamfanin Mamuda tare da ganawa da shugabannin wurin don habaka kasuwanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.