Kirisimeti: Gwamna Ya Gwangwaje Ma'aikata da Kudin Hutu, Zai Raba Masu N150,000
- Ma'aikatan Ebonyi za su gudanar da bukukuwan krisimeti da karshen shekara a cikin walwala bayan kyautar gwamnati
- Gwamnan jihar, Francis Nwifuu zai raba kyautar N150,000 ga dukkanin ma'aikatan jihar domin su dan sarara lokacin bikin bana
- Babban mai magana da yawun Nwifuru, Monday Uzor ya tabbatar wa da ma'aikatan cewa kyautarsu za ta sauka ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ebonyi - Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya sanar da bayar da gagarumar kyauta ga ma’aikatan da ke fadin jihar a matsayin ‘kyautar kirisimeti.’
Gwamnatin jihar ta sanar da ware kudade, inda za a ba kowane ma’aikacin gwamnatin jihar ₦150,000 don jin dadin bukukuwan kirisimeti da na karshen shekara.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa babban sakataren yada labaran gwamnan, Monday Uzor, ne ya bayyana hakan a cikin wani rubutu da ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna zai ba ma’aikata kyautar kudin kirismeti
Gwamna Francis Nwifuru ya tabbatar wa da ma’aikatan jiharsa ta Ebonyi cewa kyautar kudi, N150,000 da ya yi masu alkawari zau sauka a akawun dinsu a ranar Talata, 17 Disamba, 2024.
Monday Uzor ya wallafa cewa:
“Duk wani ma’aikaci a jihar Ebonyi zai karɓi ₦150,000 a matsayin kyautar kirisimeti kafin karfe 1.00 na ranar Talata… Gwamna Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru.”
Gwamna ya amince da mafi karancin albashi
Tun a watan Oktoba gwamnan ya amince da biyan ma’aikatan Ebonyi mafi karancin albashi ₦75,000 domin daga likkafar ma’aikatan jihar.
An fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin, wanda gwamnan ya ce ya biyo bayan nazari da aka yi kan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.
Gwamna ya yi barazana ga ma'aikata
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru ya gargadi ma'aikatan jihar da su ka biye wa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) cewa za su iya rasa aikinsu.
Gwamna Nwafuru ya bayyana cewa bai ga dalilin da zai sa ma'aikatan jihar su tsunduma yajin aikin da NLC ta kira ba, ganin cewa tuni ya amince da biyan N75,000 ga ma'aikata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng