Majalisar Tarayya Za Ta Binciki yadda Gwamnatin Buhari Ta Kashe Bashin $232m

Majalisar Tarayya Za Ta Binciki yadda Gwamnatin Buhari Ta Kashe Bashin $232m

  • Majalisar wakilan kasar nan ta bayyana damuwa bisa yadda ake samun karuwar matsalar abinci mai gina jiki a Najeriya
  • 'Dan majalisa mai wakiltar Imo, Chike Okafor ya bayyana cewa akwai alamun an yi almundahana a shirin inganta bangaren
  • An kafa kwamitin da zai bibiyi yadda aka kashe bashin Naira biliyan 350 da aka karbo daga Bankin Duniya domin magance matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Majalisar Wakilai ta yanke shawarar bincikar zargin almubazzaranci na bashin Naira biliyan 350 da Bankin Duniya ya ba gwamnatin Buhari don shirin inganta abinci mai gina jiki.

Majalisa
Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Majalisar ta dauki matakin e ta biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa na jam'iyyar APC daga Imo, Chike Okafor, ya gabatar a zaman majalisar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Batutuwa 30 sun jawo taron ECOWAS a Najeriya, ministoci sun hallara a Abuja

Jaridar Punch ta wallafa cewa shirin ANRIN wani yunƙuri ne da Bankin Duniya ya ɗauki nauyi domin magance matsalolin abinci mai gina jiki a Najeriya da bashin $232m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin gwamnatin Buhari da almundahana

Jaridar Leadership ya wallafa cewa shekarar 2018 ne aka kaddamar da shirin ARIN da nufin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki kafin wa’adin watan Disamba 2024.

Sai da Hon. Okafor ya bayyana damuwa cewa, duk da kyawawan manufofin shirin, bai cimma nasara ba, saboda rahotanni sun nuna nuna matsalolin abinci mai gina jiki suna ƙara kamari.

Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari

Majalisar wakilai ta amince da kudirin da zai binciki zargin barnatar da bashin da Bankin Duniya ya bayar domin a magance matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Bayan amincewa da kudirin, Majalisar ta umarci kwamitocin gina jiki da tsaro na abinci, Kudi, tallafi, rance da gudanar da bashi su gudanar da binciken.

Kara karanta wannan

An gano inda Tinubu ya 'tura' kudin da aka tara bayan cire tallafin man fetur

Haka kuma, an umurci waɗannan kwamitocin su gayyaci ma’aikatar lafiya ta tarayya, hukumar raya kiwon lafiya a matakin farko, Bankin Duniya, jihohi 12 masu cin gajiyar shirin.

Basarake ya yabi mulkin Muhammadu Buhari

A baya, mun ruwaito cewa fitaccen basaraken a kasar Yarbawa, Oba Adeyeye Ogunwusi ya yi tattaki har Daura da ke Katsina domin mika gaisuwar ban girma ga Muhammadu Buhari.

Basaraken ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya yi kokar ainun a lokacin da ya ke jagorancin Najeriya, kuma bayan mulkin, sai murmurewa ya ke yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.