Majalisar Shura: Abba Ya Rabawa Malaman Musulunci kusan 50 Mukamai a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da nada 'yan majalisar Shura ta Kano mai kunshe da manyan malamai da masana
- Farfesa Shehu Galadanci ne zai jagoranci majalisar, yayin da Gwani Shehu Wada Sagagi zai kasance sakataren majalisar
- Majalisar ta kunshi mutum 46, ciki har da fitattun malamai da manyan shugabanni, tare da burin tabbatar da zaman lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A wani mataki na tabbatar da hadin kan al’umma da inganta tsarin mulki, gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sanar da nada 'yan majalisar Shura ta jihar.
An tsara majalisar domin bayar da shawarwari kan al’amuran da suka shafi tattalin arziki, zamantakewa, da addini, tare da tabbatar da ingantaccen jagoranci a jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook ta ce majalisar ta kunshi manyan malaman addini, masana kimiyya, da shugabanni.
Shugabannin majalisar shura ta Kano
Farfesa Shehu Galadanci ne aka nada a matsayin shugaban Majalisar, yayin da Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen zai kasance mataimakinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A gefe guda, Gwani Shehu Wada Sagagi, wanda ya kasance sakataren majalisar, zai kula da gudanarwar kwamitin tare da tabbatar da aiki cikin tsari.
Daga cikin fitattun malamai da aka nada akwai Sheikh Abdulwahab Abdallah, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, Dr Bashir Aliyu Umar da Sheikh Tijjani Bala Kalarawi.
Aikin majalisar shura ta jihar Kano
Sanusi Bature ya tabbatar da cewa kwamitin zai rika bayar da shawarwari kan manyan al’amuran jihar.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa nadin ya biyo bayan hangen nesansa na tabbatar da jagoranci mai ma’ana wanda zai inganta zamantakewa tare da mutunta al’adun jihar.
Ana sa ran cewa majalisar za ta taka rawar gani wajen tsara manufofi da dabarun da za su inganta rayuwar jama’ar jihar Kano.
Jerin sunayen 'yan majalisar shura ta Kano
Shugaban majalisar shura ta Kano
1. Farfesa Shehu Galadanci
Mataimakin shugaban majalisar shura ta Kano
2. Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen
Mambobi majalisar shura ta Kano
3. Sheikh Wazirin Kano
4. Sheikh Abdulwahab Abdallah
5. Malam Abdullahi Uwais
6. Sheikh Karibullah Nasiru Kabara
7. Dr Bashir Aliyu Umar
8. Sheikh Shehi Maihula
9. Sheikh Tijjani Bala Kalarawi
10. Farfesa Umar Sani Fagge
11. Dr Muhammad Borodo
12. Sheikh Sayyadi Bashir Tijjani
13. Farfesa Muhammad Babangida
14. Sheikh Nasidi Abubakar Goron-Dutse
15. Khalifa Sukairaj Salga
16. Sheikh Hadi Ibrahim Hotoro
17. Khalifa Tuhami Atiku
18. Sheikh Nasir Adam
19. Prof. Salisu Shehu
20. Sheikh Muhammad Bin Othman
21. Sheikh Musal Kasiyuni
22. Dr Muhammad Tahir Adamu
23. Sheikh Liman Halilu Getso
24. Malam Abdurrahman Umar
25. Malam Ado Muhammad Dalhatu
26. Abdullahi Salihu Aikawa
27. Dr Nazifi Umar
28. Sheikh Abubakar Kandahar
29. Sheikh Umar Sanji Fagge
30. Sheikh Sani Shehu Maihula
31. Malam Kabiru Dantaura
32. Sheikh Sammani Yusuf Makwarari
33. Khalifa Abdulkadir Ramadan
34. Malam Nura Adam
35. Malam Ado Muhammad Baha
36. Malam Nura Arzai
37. Malam Saidu Adhama
38. Malam Sani Umar R/Lemo
39. Khalifa Hassan Kafinga
40. Gwani Ali Haruna Makoda
41. Sheikh Auwal Tijjani
42. Manjo General Muhammad Inuwa Idris
43. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
44. Alhaji Sabiu Bako
45. Alhaji Muhammadu Adakawa
46. Gwani Shehu Wada Sagagi (Sakataren Majalisa)
A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya sauke sakataren gwamnati da kuma rusa ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.
Legit ta wallafa cewa gwamnan ya yi sauye-sauyen ma’aikatu tare da sake nada wasu kwamishinoni a ma’aikatun jihar.
Asali: Legit.ng