Dalilin da Ya Sa Gwamnan Kano Ya Sauke Sakataren Gwamnati da Wasu Kwamishinoni 5
- Gwamnatin Kano ya magantu kan sauke wasu mukarraban gwamnati, ciki har da sakatare da wasu kwamishinoni biyar
- Gwamna Abba Yusuf, ya bayyana cewa an sauke mutanen ne domin tabbatar da ci gaba da inganta ayyukan gwamnati a Kano
- An sauyawa wasu kwamishinoni wuraren aiki, ciki har da mataimakin gwamna wanda ya koma ma’aikatar ilimi mai zurfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya bayyana dalilin da ya sa ya sauke sakataren gwamnati, shugaban ma'aikatar fadar gwamnati da wasu kwamishinoni biyar.
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Abba ya yi garambawul a majalisar zartarwarsa a ranar Alhamis, 12 ga watan Disambar 2024.
Abba ya magantu kan garambawul a Kano
Gwamnan, ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a wata zantawa da BCC Husa, ya ce an sauke mukarraban ne saboda yin wasu gyare-gyare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai girma Abba Yusuf ya shaida cewa aikin gwamnati yana da lokaci, kuma a matsayinsa na gwamna yana da ikon da zai nada ko ya sauke masu mukamai.
Sanusi Bature ya ce:
"An yi wannan gyare-gyare ne don tabbatar da ayyuka da kuma yadda mulkinsa ke gudana ta yadda zai samu damar ci gaba da taimakawa al'ummar jihar."
Me ya sa gwamnan Kano ya sauke mutanen 7?
Da aka tambayi Sanusi Bature dalilin da ya sa gwamna Abba Yusuf ya sauke mukarraban nasa bakwai, sai cewa ya yi:
"A cikinsu babu wanda ya yi laifi, kuma babu wanda ba ya aikinsa daidai gwargwado. Sai dai kawai shi gyara idan ya tashi ana yinsa ne a daidai lokacin da ya kamata.
"Haka suma wadanda aka canjawa ma'aikata, an kalli kowane aka ga kwazonsa, aka gano inda ya fi dacewa da su, shi ya sa aka canja masu wajen aiki."
An sauyawa kwamishinoni wuraren aiki
Mai magana da yawun Gwamna Abba, ya yi bayani kan kwamishinonin da aka sauyawa wuraren aiki da suka hada da mataimakin gwamnan jihar.
"Mataimakin gwamnan jihar shi ne kwamishinan kananan hukumomi ya koma ma'aikatar ilimi mai zurfi, sannan kwamishiniyar jin kai ta koma ma'aikatar mata.
"Ita kwamishiniyar mata ta koma ma'aikatar yawon bude ido da raya al'adu. Akwai kusan kwamishinoni guda 10 da aka sauyawa wuraren aiki."
Gwamnatin Kano ta yi sababbin nade nade
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sababbin nade nade a bangarorin shari'a, zakka da hubusi da kuma hukumar ma'aikatan Kano.
Yayin da gwamna ya ce ya yi nade-naden ne bisa tsarin doka, ya kuma tabbatar da cewa nadin mutane zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnatinsa a jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng