Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'adda a Wani Artabu, Sun Kwato Makamai
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun yi arangama da ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan ne a ƙauyen Bambaran da ke ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara
- Jami'an tsaron tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun hallaka ƴan ta'adda tare da ƙwato makamai daga hannun miyagun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun hallaka ƴan ta'adda a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na Askarawan Zamfara (ZSCPG) da ƴan banga sun yi arangama da ƴan ta'addan ne a ƙaramar hukumar Anka.
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda a Zamfara
Majiyar ta bayyana cewa sojojin sun fafata da ƴan ta'addan ne a ƙauyen Bambaran da ke ƙaramar hukumar Anka.
A sakamakon musayar wutar, dakarun sojojin sun samun nasarar hallaka ƴan ta'adda guda biyu.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai da suka haɗa da babbar bindiga ƙirar PKT, AK-47 guda ɗaya, jigida guda ɗaya da harsasai na musammna guda uku masu kaurin 7.62mm.
Wannan nasarar ta nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da tsaro a jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.
Karanta wasu labaran kan sojoji
- 'Yan bindiga sun shiga uku, sabon hafsan rundunar sojojin Najeriya ya kama aiki
- Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an kwato motar 'yan ta'adda
- Sojoji sun yi ruwan bama bamai kan ƴan bindiga a Arewa, an kashe miyagu masu yawa
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da miyagu inda suka samu nasarar kashe ƴan ta’adda da dama a Zamfara.
Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne masu tayar da ƙayar baya a wani samame da suka kai maɓoyarsu da ke a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng