Jerin Ƴan Najeriya 7 da Ke Riƙe da Manyan Mukamai a Hukumomin Duniya

Jerin Ƴan Najeriya 7 da Ke Riƙe da Manyan Mukamai a Hukumomin Duniya

'Yan Najeriya da dama na riƙe da manyan mukamai a kungiyoyin kasa da kasa, inda suke ba da gudummuwa a fannonin kasuwanci, kudi, gwamnati da sauransu.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohuwar ministar kuɗi a Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, Akinwumi Adesina da Amina Mohammed na cikin manyan ƴan Najeriya da ke riƙe da manyan muƙamai a duniya.

Dr. Ngozi, Akinwumi Adesina da Amina Muhammed
Yan Najeriya da ke rike da manyan muƙamai a duniya Hoto: @wto, Akinwumi Adesina, @AminajMohammed
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ayyukan waɗannan mutane ƴan asalin Najeriya a wurare daban-daban a duniya yana ƙara ɗaga ƙimar Afirka da bunƙasa tattalin arziki.

Legit Hausa ta zaƙulo maku jerin ƴan Najeriya bakwai da yanzu haka suke riƙe da muƙamai a duniya, ga su kamar haka:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Shugabar WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala

Ngozi Okonjo-Iweala fitacciyar masaniyar harkokin tattalin arziki ce daga yankin Ogwashi-Ukwu, jihar Delta a Najeriya, an haife ta a ranar 13 ga Yuni 1954.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojoji suka hallaka 'yan ta'adda 181 yayin artabu

Yanzu haka dai Dr. Ngozi ce Darakta Janar watu shugabar ƙungiyar cinikayya ta duniya watau WTO. Ta hau wannan muƙami a karon farko a shekarar 2021.

A watan Nuwamba, 2024, ƙungiyar WTO ta sanar da sake naɗa tsohuwar ministar a matsayin Darakta-Janar karo na biyu a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X.

2. Shugaban bankin AfDB, Akinwumi Adesina

Akinwumi Adesina ya kasance shugaban bankin raya Afirka (AfDB) tun a 2015 kuma an sake zaben shi zango na biyu na shekaru biyar a 2020.

An haifi Adesina a ranar 6 ga Fabrairu 1960, mahaifinsa wani manomi ne dan Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

A karkashin jagorancinsa, bankin AfDB ya bullo da shirye-shirye kamar 'High 5s Strategy'. Akin Adesina ya taɓa riƙe ministan noma da raya karkara na Najeriya a 2010.

3. Majalisar dinkin duniya, Amina J. Mohammed

UN ta wallafa a shafinta ranar 3 ga watan Janairu, 2017 cewa sakataren majalisar ɗinkin duniya ya naɗa Amina J. Muhammed a matsayin mataimakiyarsa.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu ya naɗa shi muƙami, tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya fice daga PDP

Tun daga 2017, Amina Mohammed ke rike da wannan kujera ta mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (UN).

Haka nan ta jagoranci kungiyar samar da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke tafiyar da harkokin hukumomin UN da dama.

An haifi Amina Mohammed a birnin Liverpool na kasar Ingila a ranar 27 ga watan Yuni 1961, mahaifinta wani Hausa-Fulani ne dan Najeriya.

Kamar dai sauran da muka kawo maku a sama, Amina ta riƙe mukamin ministar muhalli ta Najeriya.

4. Shugaban Afrexibank, Benedict Oramah

Farfesa Benedict Oramah, wanda aka haifa ranar 24 ga watan Yuli, 1961 a jihar Ribas, shi ne shugaban bankin safarar kayayyaki na Afirka (Afreximbank) tun 2015.

Masu hannun jari a Afreximbank sun sake naɗa Oramah karo na biyu a matsayin shugaban bankin a watan Yunin, 2020, kamar yadda bankin ya wallafa a shafinsa.

Mista Oramah ya ba da gudummawa ga shirye-shiryen kasa da kasa da dama da nufin bunkasa tattalin arzikin Afirka.

Kara karanta wannan

"Kwaɗayin mulki": An faɗi wasu manyan ƴan siyasa a Arewa da ke taimakawa ƴan bindiga

5. Kungiyar Injiniyoyin duniya, Mustafa Balarabe Shehu

Injiniya Mustafa Balarabe Shehu ɗan asalin Najwruya shi ne baƙar fata na farko da ya rike mukamin shugaban kungiyar Injiniyoyi ta Duniya (WFEO).

An haifi Mustapha a ranar 12 ga Afrilu, 1963 a jihar Kano da ke shiyyar Arewa maso Yammacin Nigeria.

6. Wale Edun

Wale Edun shi ne dan Najeriya na farko da ya hau kujerar shugaban kungiyar gwamnonin Afrika ta bankin duniya a 2023 cikin shekaru 60.

Yanzu haka dai Edun shi ne ministan kudi da harkokin tattalin arziki a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Edun ya kasance shugaban kungiyar tattalin srzikin ƙasa ta Najeriya (NESG) kuma kwanan nan aka nada shi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Afirka na Bankin Duniya.

7. Fatima Kyari Mohammed

Kamar yadɗa yake a shafin UN, Fatima Kyari Mohammed ce babbar mai sa ido ta Majalisar dinkin duniya a kungiyar tarayyar Afirka watau AU tun daga 2018.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

Ta kuma riƙe muƙamin daraktar hukumar warware rikice-rikice da tsaron yammacin Afirka daga baya ta koma ƙungiyar raya kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a matsayin babbar mai ba da shawara ta musamman.

Kasashen da ba a Kirismeti da sabuwar shekara

A wani labarin, kun ji cewa akwai ƙasashe waɗanda ba su gudanar da bikin murnar ranar Kirismeti da sabuwar shekara.

Legit Hausa ta tattaro maku irin waɗannan ƙasashen waɗanda ba su ba da hutu a ranar Kirismeti domin gudanar da bukukuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262