Hadimin Akpabio Ya Nemi Yafiyar Gwamna bayan Ya Taya Shi Murnar Mutuwar Matarsa
- An yi ta sukar Sanata Godswill Akpabio bayan hadiminsa ya yi katobara game da mutuwar matar gwamna
- Hadimin Akpabio mai suna Uduak Udo ya nemi yafiyar Gwamna Umo Eno kan kuskuren taya shi murnar mutuwar matarsa
- Hakan ya jawo ka-ce-na-ce a kafofin sadarwa inda ake amfani da shi wurin sukar Sanata Godswill Akpabio
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hadimin Sanata Godswill Akpabio ya nemi afuwar Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom.
Mr. Uduak Udo ya nemi yafiyar ne bayan taya gwamnan murnar mutuwar matarsa da ta rasu a watan Satumbar 2024.
Hadimin Sanata Godswill Akpabio ya yi katobara
Premium Times ta ce an yi ta sukar Akpabio kan katobarar da hadiminsa ya yi a wani taro a birnin Uyo da ke Akwa Ibom.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafin Facebook, Udo ya ce:
"Ina taya mai girma gwamnan jihar Akwa Ibom game da mutuwar matarsa."
Mr. Udo ya nemi afuwar Gwamna Umo inda ya ce ya so taya shi murna ne kan mutunta matarsa da ya binne ta yadda ya kamata.
Hadimin Akpabio ya nemi afuwar gwamna kan kalamansa
"Wannan subutar baki ne, hakan na faruwa idan tunaninka da abin da ka furta ya bambanta."
"Ina mai ba gwamna Eno hakuri kan wannan abin da ya faru da kuma mai gida na da aka jingina kuskuren da ofishinsa."
- Uduak Udo
Udo ya kuma nemi afuwar yan uwansa da abokan arziki kan katobarar da ya yi inda ya bukaci addu'o'insu game da halin da ya shiga.
Hadimin gwamna ya yi murabus
Kun ji cewa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya rasa hadiminsa na musamman da ya dade yana aiki a gidan gwamnatin jihar.
Hadiminsa a bangaren wayar da kan al'umma, Aniekeme Finbarr ya yi murabus daga mukaminsa domin neman sauya layi.
Wannan na zuwa ne yayin da ake jimamin mutuwar matar gwamnan wacce ta rasu a watan Satumbar 2024 da muke ciki.
Asali: Legit.ng