Abba Ya Sauke Sakataren Gwamnati, Baffa Bichi, Sagagi da Kwamishinoni 5 a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Sakataren Gwamnati (SSG) da kuma rusa ofishin Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnati (COS)
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya yi sauye-sauyen ma’aikatu tare da sake nada wasu kwamishinoni a ma’aikatu daban-daban
- Wasu kwamishinoni guda biyar an sauke su daga mukamansu tare da umarnin su gabatar da kansu a ofishin gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da sauye-sauye a majalisar zartarwa domin tabbatar da ingantaccen aiki a gwamnatinsa.
Wannan shi ne karo na farko da gwamna Abba Kabir Yusuf ke yin irin wannan babban sauyi tun bayan hawan gwamnatinsa.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya wallafa a Facebook ta ce sauye-sauyen za su fara aiki nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sauke sakataren gwamnatin Kano
Abba Kabir Yusuf ya rusa ofishin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Alhaji Shehu Wada Sagagi, sannan ya sauke sakataren gwamnati, Dr Abdullahi Baffa Bichi, bisa dalilan rashin lafiya.
A cewar sanarwar, wasu kwamishinoni da shugabanni sun sake samun mukamai a ma’aikatu daban-daban, yayin da wasu biyar aka cire su daga mukamansu.
Daga cikin wadanda aka sauke sun haɗa da:
- Ibrahim Jibril Fagge (Kwamishinan kudi)
- Ladidi Ibrahim Garko (Kwamishinar al’adu)
- Baba Halilu Dantiye (Kwamishinan yada labarai)
- Shehu Aliyu Yammedi (Kwamishinan ayyuka na musamman)
- Abbas Sani Abbas (Kwamishinan cigaban karkara)
Kwamishinonin da suka tsira da mukamansu
Daga cikin waɗanda suka tsira da mukamansu sun haɗa da Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Isa Dederi, da Kwamishinan Lafiya, Dr Abubakar Labaran.
Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulssalam zai cigaba da lura da ma’aikatar ilimin manyan makarantu.
A cikin waɗanda aka sauyawa ma'aikata akwai Hon. Mohammad Tajo Usman daga ma'aikatar fasaha da kimiyya zuwa ma’aikatar kananan hukumomi da Sarauta.
Yiwuwar sauyawa wasu wuraren aiki
Abba Kabir ya umurci shugaban ma’aikata da sauran kwamishinonin da aka sauke su gabatar da kansu a ofishinsa domin yiwuwar sake nada su a wasu mukaman.
Sanusi Bature ya ce wannan mataki yana daga cikin kokarin gwamna na tabbatar da cewa an samu ingantaccen aiki tare da samar da ayyukan ci gaban al’umma a jihar Kano.
Abba Kabir ya nada mukamai sama da 20
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta yi sababbin naɗe-naɗe a muhimman guraben tafiyar da al'amura a jihar.
An ruwaito cewa Abba Kabir ya yi naɗin a ɓangarorin shari'a, zakka da hubusi da kuma hukumar ma'aikatan jihar Kano a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng