Gombe: An Rasa Rayuka a Rikicin Makiyaya da Manoma, An Kona Amfanin Gona

Gombe: An Rasa Rayuka a Rikicin Makiyaya da Manoma, An Kona Amfanin Gona

  • Ana fargabar rasa rayuka yayin da rahotanni suka tabbatar da rikici tsakanin makiyaya da manoma
  • Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Powishi da Kalindi da ke karamar hukumar Billiri a jihar Gombe
  • Kakakin rundunar yan sanda, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar faruwar lamarin ga wakilin Legit Hausa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - An samu rahoton cewa mutum biyu sun rasa rayukansu sakamakon rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Rikicin da aka shafe kwanaki biyu ana yi a kauyukan Powishi da Kalindi da ke karamar hukumar Billiri da ke jihar Gombe ya yi sanadin asarar amfanin gona.

An rasa rayuka yayin rikici tsakanin manoma da makiyaya
Mutane biyu sun mutu yayin rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Gombe. Hoto: Gombe Police Command.
Asali: Facebook

An rasa rayuka a rikicin manoma da makiyaya

Premium Times ta ce yan yankin sun bayyana cewa harin ya haifar da lalata amfanin gona masu muhimmanci da aka bunkawa wuta.

Kara karanta wannan

Yan sanda, sarakuna da mutanen gari sun hadu domin murkushe 'yan daba a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata a yankin, Christina Anthony ta ce rikicin ya fara ne a ranar Litinin 9 ga watan Disambar 2024.

Anthony ta ce wasu makiyaya sun farmaki wani mazaunin Kalindi da yake kan hanyarsa zuwa gona a kan babur.

“Makiyayan sun farmaki mutumin inda suka kwace babur dinsa bayan ya dawo gida ya shaidawa matasan garin abin da ya faru da shi.
“Matasan suka bi sahun makiyayan har suka dawo da babur din amma sai rikicin ya kazance a ranar Laraba lokacin da makiyayan suka dawo suka kai hari kan mazauna garin."

- Christina Anthony

Gombe: Matakin da yan sanda suka ɗauka

Kakakin rundunar yan sanda a Gombe, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Legit Hausa.

ASP Abdullahi ya ce harin ya yi sanadin mutuwar Malam Yusuf Akwara da ke kauyen Powishi da ke gundumar Kalmai a Billiri.

Ya ce kwamishinan yan sanda ya umarci tura jami'an tsaro domin duba yawan barnar da aka samu sanadin harin.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

Sai dai ya ce rundunar ta isa wurin da lamarin ya faru inda ta iske maharan sun tsere yayin da aka yi kokarin kashe wutar da aka kunna.

Rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya

Kun ji cewa an samu ɓarkewar rikici tsakanin matasa da wasu makiyaya a ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba ta jihar Gombe.

Rikicin wanda ya fara sakamakon tare hanyar da wasu matasa suka yi ya jawo mutum ɗaya ya rasa ransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.