Hamshakin Dan Kasuwar Arewa Ya Yi Gagarumar Asara, Arzikinsa Ya Ragu da $3.7bn
- Dukiyar Alhaji Abdulsamad Rabiu, shugaban rukunonin kamfanin BUA ta ragu da dala biliyan 3.7 a cikin shekarar 2024
- Abdulsamad, ya rage matsayi a jerin attajiran Afrika daga daga na biyar zuwa na shida sannan ya koma na 581 a jerin duniya
- Rahoto ya nuna cewa attajirin ya yi asarar kaso mai yawa a kamfanin abinci da na simintin BUA wanda ya shafi kasuwancinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Faduwar darajar kudin Najeriya ya yi tasiri sosai kan dukiyar fitaccen hamshakin attajirin Najeriya, Alhaji Abdulsamad Rabiu.
Abdulsamad shi ne shugaban kamfanin BUA, wanda yake daya daga cikin manyan masana'antun da ke tashe a nahiyar Afrika.
Abdulsamad Rabiu ya yi asarar $3.7bn
Bisa rahoton mujallar Forbes, darajar dukiyar Abdulsamad ta ragu daga dala biliyan 8.2 a farkon shekara zuwa dala biliyan 4.5 a Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jimlace, dukiyar mai kamfanin ns BUA daga Janairu zuwa Disambar 2024, ta ragu da dala biliyan 3.7 (kusan Naira tiriliyan 5.7), sakamakon faduwar Naira.
An rahoto cewa mafi akasarin kamfanonin da ake gudanar da su a kan Naira sun samu tawayar arziki a 2024 sakamakon faduwar Naira a kan Dalar Amurka.
Shugaban BUA ya sauko a jerin attajirai
Rahoton Billionaires Africa ya bayyana cewa yanzu Abdulsamad ne na uku a jerin attajiran Najeriya, daga matsayi na biyu a farkon shekarar 2024.
A jerin attajiran nahiyar Afirka kuwa, shugaban kamfanin BUA ya koma matsayi na shida daga na biyar, sannan ya koma na 581 a duniya.
Azikin Abdulsamad Rabiu a duniya ta yi kasa sosai, inda mujallar Forbes ta taba ayyana shi a sanya cikin attajirai 400 na duniya.
Darajar kamfanonin BUA ta ragu
An rahoto cewa Abdulsamad yana da kaso 99.8% a kamfanin BUA Foods da kaso 96.3% a kamfanin BUA Cement, babban kamfanin siminti na biyu a Najeriya.
Darajar kasuwancinsa a kamfanin BUA Foods ta ragu daga dala biliyan 5.2 zuwa dala biliyan 1.9, yayin da ta BUA Cement ta koma dala biliyan 4.5.
Wannan ragin ya samo asali ne daga faduwar darajar Naira da kuma matsalolin tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2024.
Kamfanin BUA ya yi cinikin N1trn
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin BUA foods ya samu cinikin Naira tiriliyan 1.07 daga watan Janairu zuwa Satumbar shekarar 2024.
Duk da tarin kalubalen kudi da kuma rashin kudi a hannun jama'a, kamfanin Dangote ya ce ya samu ribar kusan Naira biliyan 524.42 daga cinikin da ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng