Gwamna Radda Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatin Jihar Katsina

Gwamna Radda Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatin Jihar Katsina

  • An yi rabon kujeru a jihar Katsina yayin da Mai girma Dikko Umaru Radda ya naɗa sababbin muƙamai a gwamnatinsa
  • Radda ya naɗa sabon kwamishina da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamban 2024
  • Tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kafur/Malumfashi ya zama sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda, ya yi rabon sababbin muƙamai a gwamnatinsa.

Gwamna Dikko Radda ya naɗa Malik Anas a matsayin kwamishina, inda za a jira amincewar majalisar dokokin jihar.

Gwamna Radda ya nada kwamishina
Gwamna Radda ya yi rabon mukamai a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Gwamna Radda ya naɗa sabon kwamishina

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin kafafen yaɗa labarai na zamani, Isah Miqdad ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abba Gida Gida ya naɗa muƙamai sama da 20 a ɓangarori 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isah Miqdad ya bayyana kafin naɗin da aka yi wa Malik Anas na kwamishina, shi ne mai ba da shawara na musamman ga Gwamna Radda kan harkokin kuɗi da bankuna.

Ya bayyana cewa Malik Anas ya kuma taɓa riƙe muƙamin Akanta Janar na jihar Katsina kuma yana da digiri na biyu a fannin harkokin gudanarwa na kasuwanci daga jami'ar Bayero da ke jihar Kano (BUK).

Gwamna Radda ya naɗa sabon shugaban ma'aikata

Hakazalika, Isah Miqdad ya bayyana cewa Gwamna Radda ya amince da naɗin sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar.

A cewar Isah Miqdad, an naɗa Hon. Abdulkadir Mamman Nasir a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina.

Hon. Abdulkadir Mamman Nasir tsohon ɗan majalisar wakilai ne da ya wakilci Kafur/Malumfashi.

"Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ya amince da naɗin tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jiha (COS)."

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi wa'azi ana alhinin rasuwar shugaban karamar hukuma

-Isah Miqdad

Gwamna Radda ya gabatar da kasafin kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gabatarwa majalisar dokokin jihar kasafin kudin shekarar 2025.

Gwamna Dikko Radda PhD ya gabatar da N682,244,449,513.87 a matsayin kasafin kudin jihar Katsina na shekarar 2025 da ake tunkara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng