Kudirin Haraji: Matawalle Ya Ja Kunnen Masu Sukar Tinubu, Ya Fadi Amfanin Yin Gyaran

Kudirin Haraji: Matawalle Ya Ja Kunnen Masu Sukar Tinubu, Ya Fadi Amfanin Yin Gyaran

  • Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa manufofin Bola Tinubu kan tatttalin arziƙi sun fara haifar da ɗa mai ido
  • Matawalle ya kuma nuna goyon bayansa ga ƙudirin haraji wanda ya ce yana da amfani wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan
  • Ƙaramin ministan tsaron ya buƙaci masu sukar shugaban ƙasan da su riƙa sanya gaskiya a cikin bayanansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan sauye-sauyen da Bola Tinubu ya kawo kan tattalin arziƙin ƙasar nan.

Bello Matawalle ya ce sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya yi da manufofinsa kan tattalin arziƙi, sun fara haifar da ɗa mai ido.

Matawalle ya yabi kudirin haraji
Matawalle ya yabi manufofin Tinubu kan tattalin arziki Hoto: @DOlusegun, @BelloMatawalle1
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ma'aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar a ranar Alhamis wacce aka sanya a shafin ma'aikatar tsaro na defence.gov.ng

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Matawalle ya yaba da manufofin Tinubu

Bello Matawalle ya ce, waɗannan tsare-tsare da suka haɗa da gyara fasalin haraji da wasu muhimman nasarori da aka samu a bangarori daban-daban, sun fara farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan ƴan Najeriya, za su amfana da wannan sauyin da aka samu a fannin tattalin arziƙi.

Don haka ya buƙaci masu sukar gwamnatin Tinubu, musamman waɗanda suka fito daga wasu sassan Arewacin Najeriya da su kasance masu faɗin gaskiya a cikin sukar da suke yi.

"Dangane da sukar da ake yi, musamman daga wasu sassan Arewacin Najeriya, ina kira ga masu yinta da su kasance masu faɗin gaskiya a cikin bayanansu."

- Bello Matawalle

Matawalle ya yabi ƙudirin haraji

Da yake magana kan ƙudirin haraji, Matawalle ya bayyana su a matsayin abubuwa masu muhimmanci domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya bayyana cewa, an tsara waɗannan sauye-sauyen ne domin samar da ingantaccen tsarin haraji, wanda zai inganta samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati tare da sauƙaƙa matsalolin kuɗi ga talakawa da ƙananan ƴan kasuwa.

Kara karanta wannan

"Ba mu son kowa ya kwana da yunwa," Shugaba Tinubu ya shirya wadata abinci a Najeriya

"Ta hanyar faɗaɗa haraji tare da tabbatar da cewa kowa yana biyan kasonsa, Shugaba Tinubu yana kafa tubalin samar da tattalin arziki mai ɗorewa."
"Waɗannan gyare-gyaren ba kawai za su ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga gwamnati ba ne, za su ƙara sanya zuba jari da samar da ayyukan yi a sassa daban-daban."

- Bello Matawalle

An karrama Ministan tsaro, Bello Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya samu karramawa daga ƙungiyar International Defence Group Organisation (ICNGO).

Ƙungiyar ICNGO ta bayyana Bello Matawalle a matsayin ministan da babu kamarsa a watan Nuwamban 2024, saboda nasarorin da ya samu wajen magance rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng