Kwamitin Ɗangote, Tinubu Sun Miƙa Kayan Tallafin N1bn ga Gwamnatin Borno

Kwamitin Ɗangote, Tinubu Sun Miƙa Kayan Tallafin N1bn ga Gwamnatin Borno

  • Kwamitin shugaban ƙasa da attajirin nan, Alhaji Aliko Ɗangote sun cika alkawari ga mutanen Borno bayan ambaliya
  • An kafa kwamitin da zai tattaro tallafi domin agazawa mutanen da ambaliyar madatsar Alau ta rutsa da su a Maiduguri
  • Bayan tattaro gudunmawar, kwamitin ya miƙa abin da aka samu ga hukumar bayar da agajj ta NEMA, ta miƙa ga gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Al'ummar da mummunan ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Maiduguri, babban birnin Borno sun samu gagarumin agaji.

Kwamitin mashahurin ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote da haɗin gwiwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu sun tattaro tallafin kayan da zai amfani mutanen.

Borno
Gwamnati ta tallafawa mazauna Borno Hoto:h
Asali: Twitter

A saƙon da hukumar NEMA ta wallafa a shafin X, kwamitin shugaban ƙasa kan taimakon ambaliya da inganta rayuwa (PCFRR), ta hannun hukumar agajin gaggawa ce ta kai tallafin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da wasu gwamnoni ana tsaka da surutu kan ƙudirin Haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗangote da gwamnati sun kai agaji Borno

Kwamitin PCFRR ya bayar kayan da tallafi na ₦1bn ga gwamnatin Borno don rarrabawa ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Yayin miƙa tallafin a Maiduguri, darekta janar ta NEMA, Zubaida Umar, wacce Adamu Abdullahi Usur, ya wakilta, ya jaddada kudirin hukumar na tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Kwamitin gwamnati ya jaddada taimakon Borno

Hukumar NEMA ta bayyana cewa kayan tallafin suna cikin kokarin ci gaba da taimakawa al'ummomin da rushewar madatsar ruwa ta Alau a Maiduguri ya shafa.

Kayan da aka bayar sun haɗa da buhunan wake 4,000, kwalin taliyar yara 5,000, jarkunan man girki 500, kwalin tumatir ɗin gwangwani 1,000, katifu 3,000 da sauransu.

Gwamnati ta fara rabon tallafi a jihar Borno

A baya, mun ruwaito cewa gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jagoranci fara raba kayan tallafi ga mutanen Maiduguri da ambaliyar ruwa ta shafa.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

Gwamna Babagana Zulum ya ce za a raba tallafin ne bayan an kasa magidantan zuwa rukuni-rukuni, inda kowa zai samu tallafi dai-dai gwargwadon asarar da ya tafka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.