'Laifin Buhari ne': Lauya Ya Kare Tinubu kan Fifita Ƙabilar Yarbawa a Gwamnatinsa
- Fitaccen lauya a Najeriya, Mike Ozekhome ya caccaki tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan zargin ya lalata kasa
- Ozekhome ya ce ba laifin Bola Tinubu ba ne yadda yake ba Yarabawa manyan mukamai saboda Buhari ne ya fara yinhakan
- Hakan ya biyo bayan korafe-korafe cewa Tinubu ya mayar da komai na Yarbawa saboda yadda yake fifita su a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - 'Dan rajin kare hakkin bil'adama kuma babban lauya a Najeriya, Mike Ozekhome ya soki tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Lauyan ya ce laifin Muhammadu Buhari ne da Bola Tinubu yake ba 'yan kabilarsa ta Yarbawa manyan mukaman gwamnatin tarayya.
Ozekhome ya caccaki Buhari kan fifita yan Arewa
Ozekhome ya bayyana haka ne yayin jawabi a wani taron bita kan hakkin dan Adam da Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Duniya (IHRC) ta shirya a Abuja, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya bayyana cewa mulkin Buhari ya raba kan 'yan Najeriya ta fuskar kabilanci da kuma addini.
Dan gwagwarmayar ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne cewa shugaba Tinubu ya bi irin wannan tsari, duba da yadda ‘yan Najeriya suka karɓi hakan ba tare da yin magana ba lokacin mulkin Buhari.
Lauya ya kare Tinubu kan fifita Yarbawa
“Idan na ji yan Arewa suna korafin cewa Tinubu yana fifita Yarbawa a mukamai saboda yadda ya nada su da yawa a manyan mukaman Najeriya, eh, suna da hujja."
"Amma tambayar da zan yi ita ce: ina ku ke lokacin da Buhari, tsawon shekaru takwas, ya mayar da Najeriya ta yan Arewa?"
"Yadda Buhari ya lalata Najeriya, Wasu mutane sun kira shi ‘na mu ne’, wannan shi ne namu, ko da kuwa yana cutar da mu, hakan ba zai dame mu ba, babu wata kasa da za ta cigaba da irin wannan tunani.”
-Mike Ozekhome
An fadi yadda Buhari ya ci zaɓen 2015
Kun ji cewa tsohon shugaban NHRC, Chidi Odinkalu ya ce APC ta samu nasara a 2015 ta hanyar zanga-zanga, sai ga shi yanzu tana murkushe masu goyon bayan hakan.
Farfesa Chidi Odinkalu ya ce zanga-zanga hakki ne na al’umma ba na gwamnati ba, amma APC ta take wannan hakkin domin bukatunta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng