"Kwaɗayin Mulki": An Faɗi Wasu Manyan Ƴan Siyasa a Arewa da ke Taimakawa Ƴan Bindiga

"Kwaɗayin Mulki": An Faɗi Wasu Manyan Ƴan Siyasa a Arewa da ke Taimakawa Ƴan Bindiga

  • Ana zargin wasu ƴan siyasa da hannu a ayyukan ƴan bindigar da suka hana jama'a zaman lafiya a Arewacin Najeriya
  • Kungiyar ASoN ta bayyana cewa wasu manyan Arewa na rura wutar da rashin tsaro da nufin ɓata gwamnatin Bola Tinubu
  • Kungiyar ta magoya bayan Shugaba Tinubu ta buƙaci jami'an taaro su zaƙulo waɗannan bara gurbin mutanen domin a samu zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wata ƙungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi zargin cewa akwai hannun wasu bara gurbin ƴan siyasa a ayyukan ƴan binidga.

Kungiyar da ake kira da ASoN a taƙaice ta yi ikirarin cewa wasu ƴan siyasa da ke kwaɗayin hawa mulki ta kowane hali ne ke rura wutar matsalar tsaro a Arewa.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar magoya bayan Tinubu ta zargi wasu yan siyasa da hannu a ayyukan ƴan bindiga Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Ƴan siyasa na taimakon ƴan bindiga

Kara karanta wannan

Jigo a NNPP ya yi martani kan bukatar 'yan Arewa su hakura da karawa da Tinubu a 2027

A cewar ƙungiyar reshen Arewa maso Yamma, ƴan siyasar suna taimakawa ƴan bindiga ne domin shafawa gwamnatin Tinubu baƙin jini, Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ASoN, Hon Lukman Hamza da sakatarensa, Kwamared Aliyu Zuberu.

Kungiyar ta gargaɗi waɗanda ta kira da manyan Arewa da ba su ƙaunar zaman lafiya kuma suke son ɓata gwamnatin Tinubu, da su daina wasa da rayukan al'umma.

Ƙungiyar ASoN ya aika sako ga hukumomi

Har ila yau, ASoN ta buƙaci jami'an tsaro musamman ƴan sandan farin kaya watau DSS su tashi tsaye su bankaɗo waɗannan bara gurbin ƴan siyasa.

Kungiyar ta ce:

"Muna gargaɗi da babban murya, masu ƙulla makirci da tada hankalin al'umma don cimma burinsu na siyasa a Arewa su canza tunani tun da wuri-wuri."
"Don haka muna jan hankalin wasu manyan jiga-jigai a Arewa, waɗanda ba su son zaman lafiya kuma suke ƙoƙarin shafawa gwamnatin Tinubu baƙin jini su sani rayukan mutane suke wasa da su."

Kara karanta wannan

Zaben shugaban kasar Ghana ya sa PDP ta hango abin da zai faru da Tinubu a 2027

"An yi zabe kuma ya wuce, ya zama wajibi mu haɗu mu marawa waɗanda Allah ya ba mulki baya domin a gudu tare a tsira tare."

Ƴan Arewa sun kafawa Tinubu sharuɗɗa

Kun ji cewa manyan kungiyoyin dattawa da matasan Arewa sun magantu kan sharudan janye adawarsu kan kudirin haraji.

Kungiyoyin sun kawo sharuda na musamman ga gwamnati domin duba yiwuwar daukar matakai kan kudirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262