Yaki da Badala: Hukumar Hisbah Ta Fara Aiki Gadan Gadan, Ta Kwace Kwalayen Barasa 200

Yaki da Badala: Hukumar Hisbah Ta Fara Aiki Gadan Gadan, Ta Kwace Kwalayen Barasa 200

  • Jami'an hukumar Hisbah a jihar Sokoto sun samu nasarar ƙwace wasu katan-katan na barasa da aka shigar da ita zuwa birnin Shehu
  • Kwamandan Hisbah na jihar, Usman Jatau ya bayyana cewa har yanzu babu wanda ya fito ya ce kayayyakin da aka kama mallakinsa ne
  • Usman Jatau ya kuma bayyana cewa hukumar za ta tuntuɓi kwamishinan shari'a na jihar domin sanin matakin ɗauka na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Jami’an hukumar Hisbah reshen jihar Sokoto sun ƙwace sama da katan 200 na abubuwan da ake zargin barasa ne.

Jami'an na hukumar Hisbah sun cafke kayayyakin ne a babbar tashar mota ta Sokoto.

Hisbah ta cafke barasa a Sokoto
Hukumar Hisbah ta cafke katan-katan na barasa a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Hisbah ta cafke barasa a jihar Sokoto

Kwamandan Hisbah na jihar, Usman Jatau, ya bayyana hakan a ofishin hukumar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi wa'azi ana alhinin rasuwar shugaban karamar hukuma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Usman Jatau ya kuma baje kolin kayayyakin da aka kama waɗanda ake zargin barasa ne a ofishin hukumar.

Usman Jatau ya bayyana cewa babu wanda ya fito ya bayyana cewa kayayyakin da aka ƙwace nasa ne.

Wane mataki Hisbah za ta ɗauka?

Kwamandan na Hisbah ya bayyana cewa hukumar za ta tuntuɓi kwamishinan shari’a domin sanin matakin da za ta ɗauka na gaba.

"Bari na yi kira ga al’umma da mu ji tsoron Allah (SWT) a cikin dukkanin al’amuranmu, mu guji duk wani abu da aka haramta, kamar cuɗanya tsakanin maza da mata."
"An haramta amfani da duk wani waje ko wata maɓoya domin aikata baɗala. A kiyayi cin zarafi ko zaluntar ƴan uwa Musulmai."
"Dole ne a gudanar da dukkanin bukukuwa kamar yadda Sharia ta tanada. An haramta sayarwa ko rarraba abubuwan maye ko ƙwayoyi a wurin tarurruka."

- Usman Jatau

Hisbah ta lalata barasa a Yobe

Kara karanta wannan

Wani matashi ya daɓawa mahaifiyarsa wuƙa har lahira, ya ce ita ta hana shi arziƙi

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Yobe ta lalata kwalaben barasa sama da 170 waɗanda adadin kuɗinsu ya kai N450,000.

Hukumar Hisbah ta ƙwace kwalaben ne a ɗaya daga cikin otal ɗin da ke garin Gashua, hedikwatar ƙaramar hukumar Bade da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng