An Kama Rikakken Dan Bindiga Mai Raba Makamai a Jihohin Arewa
- Rundunar Operation Safe Haven ta rushe mafakar 'yan ta'adda a karamar Bassa ta Filato, tare da cafke dan bindiga aka fi sani da Mamman
- An kama abokin ta'addancin Mamman, Malam Alhassan Samaila, tare da kwace tarin harsasai da suka boye a wata jarkar mai
- Rundunar ta tabbatar da ci gaba da aikin fatattakar masu aikata laifuffuka a Filato da kewaye domin tabbatar da tsaro a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - Sojojin Operation Safe Haven a Jihar Filato sun samu nasarar kakkabe mafakar masu garkuwa da mutane a yankin Rafiki a karamar hukumar Bassa.
An cafke shugaban masu garkuwa da mutane, Mohammed Musa, wanda aka fi sani da Mamman, tare da abokin aikinsa, Alhassan Samaila.
Rundunar soji ta wallafa a Facebook cewa an kama miyagun ne yayin wani samame da aka kai ranar 10 ga Disamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta samu nasarar gano harsasai guda 439 da aka boye a wata jarkar mai yayin bincike a mafakar su.
Yadda miyagu ke raba makamai a jihohi
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an gano cewa wadanda aka kama suna amfani da motocin haya wajen kai makamai ga 'yan bindiga a jihohin Filato, Kaduna, da Zamfara.
“Ana ci gaba da samun bayyanai daga wadanda aka kama yayin da ake gudanar da bincike domin cafke sauran 'yan ta'addar.”
- Manjo Samson Zhakom
Rahoton Punch ya nuna cewa an samamen ne bisa umarnin hafsan sojin kasa, Laftanar Janar O.O Oluyede, domin tabbatar da tsaro yayin kakar girbin hatsi da kuma bikin Kirsimeti mai zuwa.
Rundunar soji ta yi kira ga jama’a
Rundunar ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi a yankin, tana mai bayyana cewa kayan yaki da aka kara samarwa sun taimaka wajen inganta tsaro a Filato.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su rika ba da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro domin tabbatar da ganin an kawar da masu aikata miyagun laifuffuka a jihar.
An kama masu taimakon 'yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama mutane da ake zargi da kai kayan sojoji ga ‘yan bindiga.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da kayan sojoji da na ‘yan sanda, wanda ake zargin za a mika wa ‘yan bindiga masu garkuwa a jihar Katsina.
Asali: Legit.ng