Gwamna Ya Kassara Sarki, Majalisa Ta Amince da Karawa Sarakuna Girma Zuwa Ajin Farko

Gwamna Ya Kassara Sarki, Majalisa Ta Amince da Karawa Sarakuna Girma Zuwa Ajin Farko

  • Majalisar dokokin jihar Adamawa ta gabatar da kudiri game da kirkirar sababbin sarakuna zuwa matakin ajin farko
  • Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shi ya gabatar da kudirin domin inganta shugabancin sarakunan gargajiya a jihar
  • Dokar za ta rage karfin ikon Lamidon Adamawa da kuma juya shugabancin sarakunan gargajiya duk shekara tsakaninsu domin samun daidaito

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Majalisar Dokokin jihar Adamawa ta zartas da kudirin dokar kirkirar karin masarautu da nada sabbin sarakuna ajin farko.

Sabuwar dokar da ke jiran amincewar Gwamna Ahmadu Fintiri, ta samu karbuwa ne kwanaki bayan gwamnan ya rattaba hannu kan dokar kirkirar sababbin gundumomi 83.

Sabuwar dokar masarautu za ta rage Ikon Lamidon Adamawa
Majalisar jihar Adamawa ta amince da dokar kirkirar masarautu ajin farko. Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri.
Asali: Facebook

Gwamna Fintiri zai kirkiri sababbin masarautu a Adamawa

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da Gwamna Ahmadu Fintiri ya aikawa majalisar a ranar Litinin 9 ga watan Disambar 2024, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fintiri ya bukaci su zartas da kudirin dokar da za ta ba da damar nadin da cire sarakunan gargajiya, tare da kirkirar karin masarautu a jihar.

Kudirin ya samu karatu cikin gaggawa bayan 'yan majalisar daban-daban sun tattauna ka an kudirin.

Mataimakin shugaban masu rinjaye, Ahmed Rufai shi ya fara gabatar da kudirin wanda Moses Zah da Bauna Myandassa suka mara masa baya.

Shugaban majalisar, Bathiya Wesley ya tura kudirin zuwa kwamitin kula da harkokin kananan hukumomi na majalisar don ci gaba da aiki.

Yadda dokar masarautu za ta kassara Lamidon Adamawa

Sabuwar dokar ta kwace mukamin shugaban dindindin na majalisar sarakunan Adamawa daga Lamidon Adamawa, Mustapha Barkindo.

Dokar ta tanadi cewa za a ba da mukamin shugaban sarakunan gargajiya duk shekara tsakanin dukkan sarakuna masu ajin farko.

'Yan majalisar sun ce tsarin zai tabbatar da adalci da daidaito da kuma ingantaccen wakilci a harkar shugabancin gargajiya.

Kara karanta wannan

Atiku ya dauki nauyin karatun 'ya'yan talakawa, ya raba tallafi a mahaifarsa

Jam'iyyar APC ta musanta dakatar da Binani

Kun ji cewa jam'iyyar APC ta musanta labarin da ake yaɗawa kan dakatar da Sanata Aishatu Binani da ta yi takarar gwamna zaben 2023.

Sakataren yada labaran jam'iyyar, Mohammed Abdullahi ya ƙaryata labarin, ya ce sharrin masu neman rigima ne a APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.