Hankalin Fasinjoji Ya Tashi, Jirgin Sama Ya Samu Matsala Yana Shirin Sauka a Abuja
- Fasinjojin wani jirgin kaya sun tsira daga mummunan hadari bayan daya daga na’urorin saukar jirgin ya lalace tun a sararin samaniya
- Jirgin ya sauka a yanayi mai kama da rikitowa a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba
- An gaggauta daukar fasinjoji shida da ke cikin jirgin wanda kamfanin Allied Air ya mallaka zuwa asibitin sojoji don duba lafiyarsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Jirgin saman kaya mallakin Allied Air ya rikito a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar Laraba.
Hadarin ya afku ne ne sakamakon lalacewar daya daga cikin na’urorin saukar jirgin mai dauke da rajista mai lamba 5N-JRT.
Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X cewa lamarin ya faru da misalin 10.00 na safe, kuma jirgin ya na dauke da ma’aikata shida a lokacin da ya fadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rasa rai a hadarin jirgin saman?
Daily Trust ta ruwaito cewa an samu rahoton cewa dukkannin ma’aikatan jirgin sun tsira ba tare da wani rauni ba.
Da faduwar jirhin ne aka yi gaggawar kwashe duka mutanen shida zuwa sashen lafiya na 063 na Sojojin Sama (NAF) domin duba lafiyarsu.
Ana binciken faduwar jirgin sama a Auja
Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an agajin gaggawa sun gaggauta isa wurin da jirgin ya fadi a karkashin jagorancin Kwamandan Filin Jirgin Sama na Soji (MAC) da sauran hukumomin da abin ya shafa.
Hatsarin ya sa aka rufe hanyar sauka da tashi ta filin jirgin na wucin gadi domin gudanar da bincike, wanda ya jawo tsaiko mai tsawo ga zirga-zirgar jiragen sama masu shigowa da fita.
An shawarci fasinjoji da kamfanonin jiragen sama su yi shirin fuskantar cikas har sai an bayar da sanarwa ta gaba.
Jirgin sama ya yi saukar gaggawa
A baya mun ruwaito cewa wani jirgin kamfanin Max Air ya yi saukar gaggawa a jihar Borno, bayan da daya daga cikin injinansa ya kama da wuta jim kadan bayan ya tashi.
Wasu ma’aikatan jirgin da su ka ba bayar da tabbacin lamarin sun ce injin ya kama da wuta ne bayan ya ci karo da tsuntsu, lamarin da ya sa dole matukin ya dauki matakin kare rayuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng