Ba a Gama da Rashin Tsaro ba, Hukumar NHRC Ta Gano Babbar Matsala a Zamfara
- Ana tsaka da fama da rashin tsaro, hukumar NHRC ta ce an samun karuwar take hakkokin dan Adam a jihar Zamfara
- A bikin ranar kare hakkokin dan Adam na 2024, hukumar NHRC ta ce an samu kararrakin take hakkin dan Adam sama da 120
- Sarkin Gusau ya bukaci al'ummar jihar da su girmama juna, su taimaka wa mabukata, tare da ba su sakon da za su isarwa kowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Hukumar kare hakkokin dan Adam ta Zamfara ta bayyana damuwa kan karuwar take hakkin dan Adam da aka samu a jihar a shekarar 2024.
Wannan dai na zuwa ne yayin da jihar Zamfara ke fama da hare-haren 'yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Hukumar NHRC ta yi gangami a jihar Zamfara
Abdullahi Abubakar, shugaban NHRC na jihar, ya ce hukumar ta karbi sama da kararraki 120 na take hakkin dan adam, ciki har da cin zarafi, a cewar rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bikin 'Ranar Kare Hakkokin Dan Adam' na duniya, hukumar NHRC ta gudanar da gangami domin jaddada muhimmancin kare hakkokin jama’a a jihar Zamfara.
Gangamin wanda ya samu halartar kungiyoyin ya fara daga dandalin wasanni na 'Freedom Square', inda suka tattaka har zuwa zuwa Fadar Sarkin Gusau.
An bukaci gwamna ya aiwatar da dokoki
Abdullahi Abubakar ya bukaci gwamnati da ta fara aiwatar da dokokin da aka zartar a gwamnatocin baya don karfafa matakan kare hakkokin dan adam.
A cewarsa, wadannan dokokin za su taimaka wajen tabbatar da adalci ga wadanda aka ci zarafinsu da kuma inganta kare hakkokin al’umma gaba daya.
Sarkin Gusau ya nemi hadin kan Zamfarawa
Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello ya yaba da kokarin NHRC tare da jan hankalin jama’a da su zauna lafiya, su taimaka wa talakawa, su kuma tabbatar da adalci da mutunta juna.
Sarki Ibrahim Bello ya ce:
“Dole mu girmama junanmu, mu taimaka wa mabukata, mu tabbatar da cewa mun isar da wannan kiran ga wadanda ba su samu zuwa nan ba.”
Gangamin ya kare da kiran hukumar NHRC ga gwamnatin Zamfara da shugabannin al’umma da su fifita kare hakkin dan Adam da inganta gaskiya a jihar.
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace mutane 100
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun sace wani limami da wasu mutane sama da 100 a harin da suka kai yankin Wake da ke Zamfara.
Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa an kora limamin da mutanen sama da 100 zuwa daji kamar shanu kuma har yanzu ba a tuntubi iyalansu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng