Ma'aikacin Asibiti Ya Yi Tsintuwar N40m, Ya Maidawa Mai Su a Kano
- Wani ma'aikacin asibiti a jihar Kano ya nuna halin ƙwarai bayan ya yi tsintuwar maƙudan kuɗin da suka kai N40m
- Malam Aminu Umar ya mayar da kuɗin ga mai su jim kaɗan bayan ya dawo yana nemansu a inda ya manta da su a cikin asibitin
- Shugabannin asibitin sun bayyana cewa an tura sunan ma'aikacin ga hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano domin karrama shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Wani ma’aikacin asibiti, Malam Aminu Umar Kofar Mazugal daga ƙaramar hukumar Dala, ya mayar da kuɗaɗen da wani mutum ya manta da su.
Ma'aikacin asibitin ya mayar da kuɗaɗen ƙunshin dalar Amurka waɗanda za su kai sama da N40m, da wani mutum ya bari a asibitin Abubakar Imam Urology da ke Kano.
Jaridar Daily Trust ta ce kuɗin na Alhaji Ahmed Mohammed ne, wanda bisa kuskure ya ajiye su a cikin jaka a wurin ajiye motoci na asibitin kusa da wani masallaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ma'aikaci ya mayar da kuɗin tsintuwa
Mutumin ya ɗan zauna a wajen ne na ɗan ƙanƙanin lokaci kafin ya tashi domin hawa jirgi.
Mintuna kaɗan da tafiyarsa, wani ma’aikacin asibitin, Aminu Umar da ke aiki tare da abokan aikinsa wajen share wajen, ya gano jakar kuɗin.
Aminu Umar ya bayyana cewa bayan kusan sa’a ɗaya, sai mutumin ya dawo yana neman jakar, nan take ya mayar masa da ita.
Ya ce mutumin ya nemi ya ba shi tukuici amma bai karɓa ba. Sai dai, ya ba shi lambar wayarsa inda ya yi masa alƙawarin tuntuɓarsa idan ya dawo daga ƙasar waje.
An shirya karrama ma'aikaci mai amana
Babban daraktan asibitin, Dokta Aminu Imam Yola, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya kuma bayyana cewa, hukumomin asibitin sun miƙa sunan Aminu Umar ga hukumar kula da asibitocin jihar Kano domin karrama shi na musamman.
Direban Adaidaita ya mayar da kuɗin tsintuwa
A wani labarin kuma, kun.ji cewa wani direban Adaidaita sahu (keke Napep), ya mayar da tsabar kuɗin da fasinjansa ya manta a babur ɗinsa.
Matashin mai suna Auwalu Salisu ya mayar wa fasinjansa da N15m wanda ya manta da su bayan ya taso ɗaga ƙasar Chadi domin yin sayayya a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng