Atiku Ya Dauki Nauyin Karatun 'Ya'yan Talakawa, Ya Raba Tallafi a Mahaifarsa

Atiku Ya Dauki Nauyin Karatun 'Ya'yan Talakawa, Ya Raba Tallafi a Mahaifarsa

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kammala shirin tallafa wa makarantun gwamnati da ɗalibai a Adamawa
  • A wannar shekarar, shirin ya mayar da hankali kan makarantu 18 na yankin Ganye, inda aka raba kayan karatu da na koyarwa
  • Haka zalika, an zakulo ɗalibai 10 masu hazaka sosai, aka ba su tallafi domin ci gaba da karatu a matakai na gaba a karkashin shirin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jagoranci tawagarsa wajen gudanar da shirin tallafin ilimi mai taken 'Ranar Ilimi.'

Rahotanni na nuni da cewa Atiku Abubakar ya kafa shirin ne domin tallafa wa makarantun gwamnati da ɗalibai a jihar Adamawa.

Atiuku
Atiku ya tallafawa dalibai a Adamawa. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku Abubakar ya wallafa a Facebook cewa shirin ya mayar da hankali ne kan makarantu a yankin Ganye a wannar shekarar.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin tallafin ilimin Atiku Abubakar

Shirin tallafin na bana ya mayar da hankali ne kan yankin Ganye, inda tawagar Atiku ta ziyarci dukkan makarantu 18 na gwamnati a yankin.

A yayin ziyarar, tawagar ta raba littattafan rubutu, fensir, biro da sauran kayan koyarwa da na karatu ga ɗalibai da malamai a makarantun gwamnati.

An bayyana cewa shirin ya kasance wani bangare na kokarin inganta ilimin yara da samar da kayan aikin koyarwa ga malamai.

Atiku ya ba dalibai 10 tallafin karatu

Baya ga raba kayan karatu, shirin ya kuma zaɓi ɗalibai 10 masu hazaka daga makarantun yankin domin ba su tallafin karatu.

Rahotanni sun nuna cewa an tsara tallafin domin taimaka wa ɗaliban da aka zakulo wajen ci gaba da karatunsu a matakai daban daban.

A cikin shirin, kayan aikin koyarwa da na karatu suna zuwa hannun makarantun gwamnati domin inganta darussa da kuma taimaka wa ɗalibai su samu ilimi mai inganci.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Abin da Atiku da Obi ke shiryawa Tinubu bayan yin kura kurai a 2023

2027: Atiku ya fara maganar hadaka

A wani rahoton, kun ji cewa hadimin Atiku Abubakar, Paul Ibe ya ce Atiku da Peter Obi sun gane kuskurensu a zaben da ya gabata.

Paul Ibe ya ce Atiku Abubakar ya fara tuntuɓar ƴan adawa domin su haɗa kai wajen kwato mulki da kubutar da Najeriya daga hannun APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng