Wani Matashi Ya Daɓawa Mahaifiyarsa Wuƙa har Lahira, Ya Ce Ita Ta Hana Shi Arziƙi
- Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa ya hanyar amfani da wuƙa a kauyen Elebele da ke ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa
- An ruwaito cewa matashin mai suna Godwin ya aikata wannan ɗanyen aikin ne saboda zargin mamarsa ce ta hana shi ya yi kudi
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Bayelsa ya ce an mika lamarin zuwa ga sashin binciken manyan laifuffuka a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Wani matashi ɗan kimanin shekara 22 a duniya, Godwin ya cakawa mahaifiyarsa wuka har lahira a jihar Bayelsa.
Lamarin ya faru ne a kauyen Elebele da ke yankin ƙaramar hukumar Ogbia a Bayelsa matashin ya kashe mahifiyarsa ne saboda zargin ita ce ta hana shi yin arziki.
A cewar mazauna kauyen, Godwin ya koma gida ne makonnin da suka gabata bayan ya kwashe watanni yana zaune a garin Benin na jihar Edo, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ya faɗi dalilin kashe mamarsa
An ruwaito cewa mutanen garin sun kasu gida biyu, wasu na cewa limamin coci ya gargaɗi mahaifiyar matashin kar ta kuskure ta karɓi kyauta daga ɗanta.
Wasu kuma na yaɗa cewa tun da Godwin ya dawo gida ya fara nuna wasu halaye mara kyau, yana cewa wani ya faɗa masa mamarsa ce ta lalata kaddararsa ta hana shi yin arziki.
Shugaban matasan kauyen Elebele, Kwamared Precious Okala ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun tarar da gawar matar lokacin da suka isa gidan.
Ya ce tuni matasan garin suka kama Godwin suka ɗaure shi domin ka da ya gudu, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Yadda matashi ya daɓawa mahaifiyarsa wuƙa
"Mun samu labari cewa tun da yaron ya dawo daga garin Benin na Edo ya zo da wasu munanan halaye da ba a sans hi da su ba.
A ranar kisan, ya samu saɓani da mamarsa, ya ɗauki wuƙa ya caka mata a ciki."
"An ji matashin na cewa dama Baba ya faɗa masa mahifiyarsa ce ta hana shi yin arziki," in ji Okala.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Musa Mohammed, ya ce an miƙa lamarin sashin binciken manyan laifuffuka (SCID) don yin cikakken bincike.
Matasa sun kwace bindigar jami'in NDLEA
A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasa sun tare jami'an hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar Bayeƙsa da ke kudancin Najeriya.
An ruwaito cewa bata garin matasan sun kwace bindigar da wani jami'in hukumar NDLEA yake rike da ita kuma suka harbe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng