Tashin hankali: Wani matashi ya cakawa abokinshi kwalba a kahon zuci akan guntuwar giya

Tashin hankali: Wani matashi ya cakawa abokinshi kwalba a kahon zuci akan guntuwar giya

- Wani mutumi mai suna Jude ya rasa ransa, sanadiyyar caka mishi kwalba da wani abokinsa yayi

- Lamarin ya faru ne yayin da suke shan giya tazo karewa sai rikici ya barke akan wanda zai shanye guntuwar giyar

- Hakan shi yayi sanadiyyar abokin Jude yayi amfani da kwalbar dake hannun shi ya cakawa Jude a wuya

Wani matashi da aka bayyana sunanshi da Jude ya rasa ransa akan kwalbar giya.

A yadda rahoto ya bayyana, an cakawa marigayin wuka ne a lokacin da suke rikici da abokinshi a Fatade Street, dake Ijegun. Lamarin ya faru jiya Talata 2 ga watan Yuli, 2019.

Wani wanda lamarin ya faru a gabanshi ya bayyana cewa, abokanan sun fara cacar baki ne akan wanda zai sha guntuwar giyar da ta rage ta karshe.

KU KARANTA: Kisan kai: 'Yan sanda sun sha da kyar yayin da wasu fusatattun matasa suka kone ofishinsu kurmus (Hotuna)

Cikin kankanin lokaci cacar bakin ta juye ta zama fada, hakan ya sanya daya daga cikin abokan fasa kwalbar giyar ya cakawa Jude a wuya.

An yi gaggawar garzayawa da Jude asibiti mafi kusa, amma ana zuwa aka tabbatar da cewa ya mutu.

A lokacin aka cafke abokin nashi, aka wuce dashi ofishin 'yan sanda na Isheri Oshun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng