'Yar Uwar Gwamnan Taraba da 'Yan Bindiga Suka Harba Ta Mutu, Bayanai Sun Fito
- Kanwar gwamnan jihar Taraba, Atsi Kefas, ta mutu a Abuja sakamakon harin 'yan bindiga da ya rutsa da ita a Kente da ke Wukari
- Legit Hausa ta ruwaito cewa Atsi tana cikin motar mahaifiyar Gwamna Kefas yayin da 'yan bindigar suka harbe ta a ranar Alhamis
- Rasuwar Atsi ta jawo martani daga jama’a da dama, yayin da ake jira a ji sanarwar mutuwarta daga iyalinta a hukumance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas da iyalansa sun shiga cikin tsananin jimami na rasuwar kanwar gwamnan, Atsi Kefas.
Atsi Kefas, ta rasu ne kwanaki hudu bayan da 'yan bindiga suka harbeta a wani harin kwanton bauna da ya rutsa da ita a yankin Wukari.
'Yar uwar gwamna da aka harba ta rasu
Jaridar Premium Time ta rahoto cewa kanwar Gwamna Kefas, mai shekaru 44 ta mutu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja inda ake kula da lafiyarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun farmaki motar mahaifiyar Gwamna Kefas a kanyar Kente da ke Wukari.
Atsi tana cikin motar tare da mahaifiyarta lokacin da harbin 'yan bindigar ya sameta, a harin da ya rutsa da su a ranar Alhamis.
Bayan harin, an garzaya da kanwar gwamnan zuwa Asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Wukari kafin a dauke ta zuwa Abuja don ba ta cikakkiyar kulawa.
Mutane sun yi alhinin mutuwar Atsi
Duk da cewa iyalinta da gwamnatin jihar ba su tabbatar da rasuwarta ba, amma wata majiya daga 'yan uwanta ta bayyana cewa ta mutu a daren Litinin.
A halin yanzu, wasu mutane da dama sun rika wallafa sakonnin ta’aziyya a kafafen sada zumunta game da rasuwar Atsi Kefas.
Rasuwar ta bar jama’a cikin alhini, musamman dangane da rashin da ya biyo bayan mummunan harin da ake dangantawa da rashin tsaro.
An gano wanda ya harbi kanwar gwamna
A wani labarin na daban, mun ruwaito cewa wani jami'in dan sanda ne ya harbi Atsi Kefa, watau kanwar gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu.
Wata majiya ta shaida cewa dan sandan da ke ba da kariya ga mahaifiya da kanwar gwamnan ya harbi Atsi bisa kuskure a kokarin dakile harin 'yan bindiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng