Karfin Naira: Ƴan Canji Sun Lissafa Abubuwa 3 da Suka Jawo Dalar Amurka Ta Karye

Karfin Naira: Ƴan Canji Sun Lissafa Abubuwa 3 da Suka Jawo Dalar Amurka Ta Karye

  • Naira ta ƙaru da fiye da N280 cikin mako guda, daga N1,780 zuwa kusan N1,500, wanda ya sanya ake fatan farfadowar tattalin Najeriya
  • Aminu Gwadabe ya alakanta ci gaban da da aka samu da amincewar masu saka hannun jari da kuma tsarin bankin CBN na EFEMS
  • Kuɗaɗen da 'yan Najeriya mazauna ƙetare ke turo wa gida sun ƙara wadata a kasuwar canji, tare da rage rashin tabbas a farashin canji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rahoto ya nuna cewa Naira ta samu karuwar ƙarfi kan dala, daga N1,780 zuwa N1,500 cikin mako guda, wanda ya sa murna a Najeriya.

Wannan ci gaba ya kara nuna nasarar manufofin musayar kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN), wanda ya samu yabo daga ‘yan Najeriya.

'Yan canji sun bayyana dalilin karyewar dalar Amurka a kasuwar canji
Shugaban ABCON, Aminu Gwadabe ya yi imanin cewa tsare tsaren CBN na aiki, don haka dala ta karye a kan Naira. Hoto: Bloomberg/contributor
Asali: Getty Images

Da yake zantawa da jaridar Legit.ng, Aminu Gwadabe, shugaban kungiyar ABCON, ya yabawa gwamnatin Najeriya da CBN kan irin rawar da suka taka.

Kara karanta wannan

"Ba mu son kowa ya kwana da yunwa," Shugaba Tinubu ya shirya wadata abinci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amincewar masu zuba jari ga tattali

Aminu Gwadabe ya bayyana cewa babban abin da ya ja wannan ci gaba shi ne masu saka jaru sun dawo da amincewarsu kan tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban na ABCON ya ce sha'awar masu saka hannun jari kan takardun lamuni na gwamnati ya kawo ƙarin kwararar dala zuwa cikin kasar.

Wannan lamari ya ƙarfafa ajiyar kuɗin waje na Najeriya tare da rage raɗaɗin farashin musayar kuɗi a kasuwar canji.

Kaddamar da tsarin EFEMS na CBN

Ya bayyana cewa kaddamar da tsarin EFEMS na babban bankin Najeriya (CBN) yana daya daga cikin abubuwan da suka jawo faduwar dalar Amurka.

Tsarin EFEMS ya kawo gaskiya da bayyananniyar hanya a kasuwar musayar kuɗi, ya kuma rage hada hadar son kai da rashin gaskiya a kasuwar.

"Wannan babban ci gaba ne" in ji Gwadabe, yana mai cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da CBN ne ya haifar da wannan nasara.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun tafka asara, wuta ta babbake miliyoyin Naira a Nasarawa

Karuwar kudi a kasuwa daga ketare

Karuwar kuɗin da ‘yan Najeriya mazauna ƙetare ke turo wa gida ta tsarin fasahar zamani ya kara yawan kudin da ake juyawa a kasuwar musayar kuɗi.

Gwadabe ya ce:

"Karuwar kuɗin da ake turawa daga ‘yan Najeriya mazauna ƙetare ta hanyar fasahar zamani da IMTSOs na daya daga cikin manyan abubuwan da suka kara daga darajar Naira a kasuwar musayar kuɗi."

Gwadabe ya kara da cewa babu tsananin karancin dala a kasuwa a halin yanzu, kuma ana ganin wadatarta fiye da yadda ake bukatarta.

Kasuwar canji: Dala ta ci gaba da karyewa

Tun da fari, mun ruwaito cewa Dalar Amurka ta gamu da gagarumar koma baya wanda ake ganin shi ne mafi girma a duk tsawon shekarar 2024.

A farkon Disambar da muke ciki, dalar Naira ta ba da mamaki a kasuwannin canji da kuma bankuna a kan kimar dalar Amurka inda ta karu da kusan N280.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.