'Yan Bindiga Sun Rikita Gari da Harbi, Sun bi Gida Gida Sun Dauki Mata da Yara
- Yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Kakidawa da ke yankin Gidan Goga a jihar Zamfara, sun yi garkuwa da mutane 43
- An ruwaito cewa yawancin wadanda 'yan bindigar suka yi garkuwa da su yayin kai harin mata ne da kuma yara kanana
- Mazauna kauyen sun yi kira ga gwamnati da ta turo karin jami'an tsaro domin kare al'umma daga hare-hare a gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - A wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai a kauyen Kakidawa da ke karamar hukumar Maradun, Jihar Zamfara, an sace mutane 43.
Lamarin ya faru da misalin karfe 2 na dare a ranar Lahadi, inda mazauna garin suka tsere zuwa daji domin tsira da rayukansu.
Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun kai farmaki ne dauke da muggan makamai, suna harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa jama'a cikin tsoro da rudani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar majiyar, cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai manyan maza uku, yayin da sauran mutane 40 dukkansu mata ne da yara.
Yadda aka sace mutane 43 a Zamfara
Daily Post ta wallafa cewa wani mazaunin kauyen Kakidawa ya bayyana cewa 'yan bindigar sun bi gida-gida tsakar dare, suna kwashe mutane.
“Garin ya rude da harbe-harbe yayin da jama’a ke gudun tsira da rayukansu. Mun yi kididdiga, kuma ya tabbata mutane 43 ne suka yi batan dabo.”
- Mazaunin Kakidawa
Sai dai har yanzu babu wata magana da aka yi tsakanin iyalan wadanda aka sace da 'yan bindigar domin neman kudin fansa.
Mazauna yankin sun bayyana cewa babu cikakken tsaro a kauyen, wanda a cewarsu hakan ne ke sa irin wadannan hare-hare suka kasance masu saukin yi.
Kira ga gwamnati kan tsaro a jihar Zamfara
Mazauna kauyen sun roki gwamnati da ta turo karin jami’an tsaro domin kare su daga irin wannan bala’i a nan gaba.
Haka zalika sun yi kira da a gaggauta lalubo hanyar sakin wadanda aka yi garkuwa da su domin su dawo cikin iyalansu.
Ya zuwa yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa ba kan harin da aka kai.
Jami'an tsaro sun gwabza da 'yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa hadakar jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun fafata da wani gungun 'yan bindiga a Kebbi.
Legit ta ruwaito cewa bayan an yi musayar wuta da miyagu 'yan bidigar, jami'an tsaro sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng